Galibin wasu mutane na ganin 'yan jarida ba su cika bayar da labarai ma su daɗi ba face waɗanda suka shafi tashin hankali da tonon silili da ƙwanƙwanto da kuma na haɗurra. Wannan fahimta kuwa na da nasaba da kasa fahimtar aikin jaridar kansa da wanda ke yin sa. Ni a ganina duk wani labari da ya shafi ayyukan muggan mutane da ya munanawa mutane na gari shi zan mayarwa hankali domin fallasa mai mugunta da farantawa wanda aka zalunta. Bari mu soma da mai sauƙi kafin mu duba ma su sarkakiya. Idan haɗari ya faru, misali na mota ko jirgin sama ko na kasa ko kuma gobara ko ambaliyar ruwa; za mu bayar da labarin. Shin ka san ba muna bayar da labarin ne saboda kawai a ji an mutu ko an kaririye ko an yi hasarar dukiya ba? GA AMSA: Game da haɗari ko gobara da sauran iftila'i mu kan bayar da wannan labari saboda bayyana halin waɗanda matsalar ta rutsa da su, domin samun agajin hukumomi da masu iya tallafawa. Mu kan bayar da labarin saboda jawo hankalin hukumomin tsaro da saura...