Skip to main content

Posts

Showing posts from March, 2022

Kwankwaso Ya Fice Daga PDP

Getty images Labarin da ke shigo muna yanzu haka sun tabbatar da tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fitar da sanarwar ficewa daga jam'iyyar ta PDP zuwa sabuwar jam'iyyar NNPP, jim kadan bayan da kotu ta bayar da umurnin dakatar da helkwatar jam'iyyar PDP ta kasa daga rusa membobin kwamitin zartaswar jam'iyyar reshen jahar Kano.

An Zabi Abdullahi Adamu Shugaban Jam'iyyar APC

Getty images Jam'iyyar APC ta cimma matsayar zabar tsohon gwamnan jahar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Adamu, a matsayin sabon shugabanta. Kimanin 'yan takara shida ne suka janye daga neman mukamin, da suka hada da tsohon gwamnan jahar Nasarawa Alhaji Tanko Almakura da tsohon gwamnan jahar Borno Ali Modou Sheriff da tsohon gwamnan jahar Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar Mafara da sauran su. Tun da farko dai an bayyana Abdullahi Adamu a matsayin dan takarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke marawa baya.

Sabon Rikici: Bangaren Abdul'aziz Yari Ya Aike Ma Buhari Sako Mai Zafi

A wani abinda ake ganin bai rasa nasaba da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nace akan samar da maslaha a zaben shugaban jam'iyyar APC na kasa maimakon gudanar da zabe, ya sa bangaren Abdul'aziz Yari, tsohon gwamnan jahar Zamfara ya fito fili yana Allah wa dai da matakin shugaban kasa. Yanzu haka jam'iyyar APC na ci gaba da gudanar da babban taronta na kasa a Abuja. Ku latsa hoton da ke kasa don sauraren kalaman bangaren na masu goyon bayan Yari:

An Hana Masu Mukaman Siyasa Jefa Kuri'a A Babban Taron APC Na Kasa

Kwamitin tsare-tsare na musamman na riko na jam’iyyar APC ya kori masu rike da mukaman siyasa daga kada kuri’a a babban taron kasa na ranar Asabar. A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana karara cewa “dukkan wadanda aka nada a siyasance da aka zaba a matsayin wakilai a babban taron kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 26/3/2022, ba za su kada kuri’a ba bisa la’akari da cece-kucen da ke tattare da sashe na 84 (12) na dokar zabe.  2022." KUNA IYA KARANTA:  https://tantabaranews.blogspot.com/2022/03/dole-mai-son-tsayawa-takara-ya-sauka.html Komitin, duk da haka, ya bayyana cewa masu nadin siyasa na iya halarta a matsayin masu sa ido kawai amma kada su dada kada su rage. Hakan ya biyo bayan amincewar da Majalisar Dokoki ta kasa baki daya ta yi da dokar gyaran dokar zabe da shugaban kasa Muhammadu ya sanya wa hannu Alamu sun bayyana a ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa da gwamnonin jam’iyyar APC suka amince da batun fitowar jami’an...

Kotu Ta Tabbatar Da Isah Sadik Achida Matsayin Shugaban Jam'iyyar APC Na Jahar Sokoto

Babbar kotun daukaka kara ta kasa mai mazauninta a Abuja ta tabbatar da Alhaji Isah Sadik Achida a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jahar Sokoto. An dai shafe wata daya ana jayayya a kotu tsakanin Alhaji Isah Sadik Achida da bangaren Mainasara Abubakar da ke tare da Alhaji Abdullahi Salame sai kuma bangaren shugaban majalisar dokoki ta jahar Sokoto Hon. Aminu Manya Achida. Idan ana iya tunawa dai babban mai saka kara na kasa kuma ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami SAN, ya taba wani ikirari na cewa kotu za ta tabbatar da shugabancin ga Mainasara Abubakar da ke bangaren Hon. Abdullahi Salame, wanda wannan hukuncin ya zama tamkar watsa kasa a fuskar ministan shari'ar da ya yi riga malam masallaci gabanin hukuncin kotu.

Sabuwar Dambarwar Shugabancin APC

Kwana biyu kafin ta gudanar da babban zabenta na kasa, jam'iyyar APC ta sake tsunduma wata sabuwar turka-turka game da makomar wanda za a zaba matsayin sabon shugabanta. A wata hira da BBC Hausa, gwamnan jahar Kebbi Abubakar Atiku Bagudo, wanda kuma shi ne shugaban gwamnonin APC na kasa ya ce yanzu haka sun kasa cimma matsaya akan wanda zai zama shugaban jam'iyyar a ranar asabar mai zuwa. Bagudo ya kara da cewa sun gana da shugaba Muhammadu Buhari akan samar da matsaya, amma kuma sun lura cewa da wuya idan ba zabe za a gudanar ba a maimakon samar da maslaha. Da aka tambai shi ba ya ganin samar da maslaha tamkar an tilastawa wani ne bin abinda ba ya so, shugabana kungiyar gwamnonin ya ce zai yuwu a sulhunta amma idan hakan ta gagara za a bi hanyar da za ta kawo mafita. Sai dai bai yi cikakken bayani akan wace hanya ce da za a bi idan har an kasa yin sulhu tsakanin 'yan takara. Ga alama wannan na nuna irin yadda jam'iyyar za ta fuskanci kalubale gabanin ko ba...

An Tilas Ni Tsayawa Takara - In Ji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana bukatar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a karo na biyar, in da ya ce ya wajaba ne ya karba kiran jama'a. Atiku ya yi wannan magana ne a birnin tarayya Abuja lokacin da ya ke sanar da muradin nasa, "Abubuwan da suka ja hankalina na da yawa, muhimmai daga cikin su akwai bukatar samar da hadin kai, tsaro da tattalin arziki, ciyar da bangarorin gwamnatin tarayya gaba da sauran su". Atiku Abubakar na bayyana wannan ne daidai lokacin da gwamnan jahar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa Aminu Waziri Tambuwal shi ma ya bayyana anniyarsa ta tsayawa neman shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar ta PDP. Tambuwal ya ce babu wani da ya fi dacewa ya mulki kasar nan a wannan lokaci da ake ciki idan ba shi ba. Ya bayyana kan sa a matsayin matashi kuma wanda ya goge a harkar siyasa masanin dubarun mulki da ya san makomar Najeriya...

Dole Mai Son Tsayawa Takara Ya Sauka - 'Yan Majalisar Najeriya

'Yan majalisar dattawa da na wakilan Najeriya sun hada guiwa in da suka gudanar da zaman majalisar ranar laraba 22.03.2022 a zaure guda, domin kalubalantar wani hukucin da ke barazana ga dokar da suka kaddamar. Mahukuntan sun yi watsi da hukuncin babbar kotun tarayya reshen jahar Abiya, da ta umurci ministan shari'a Abubakar Malami ya goge sashe na 84 (12) na kundin tsarin mulkin 1999, wanda ya haramta ma masu rike da mukamin siyasa tsayawa takara ko jefa kuri'a, kuma ya wajabta ma duk wanda ke neman a zabe shi a 2023 da ya sauka wata shida kafin zabe. Wannan ya jawo cece-ku-ce har ta kai shugaban kasa neman su yi ma dokar kwaskwarima, abinda kuma su ka ki amincewa da shi. A makon jiya dai babban mai sa kara na kasa, Abubakar Malami ya fito ya nuna amincewa da hukuncin babbar kotun, in da ya dauki alkawarin goge dokar. To amma kuma masana harkar shari'a sun yi ca kan wannan hukuncin tare da cewa ya sabawa doka. Fitaccen babban lauyan Najeriya Femi Falana, ya...

Shugaba Buhari Ya Dawo Najeriya

Bayan shafe 'yan kwanaki a birnin Landan na Burtaniya in da aka duba lafiyarsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya a sauka Abuja yau da dare.

Malami Ya Ce Zai Bi Umurnin Kotu Ya Goge Sashe na 84 (12)

Ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami ya ce cikin gaggawa zai bi umurnin wata babbar kotun Najeriya da ta bukaci a goge sashe na 84 da ya tilasta duk masu rike mukaman siyasa aje mukamansu kwana 30 kafin zabe. KUNA IYA KARANTA: http://tantabaranews.blogspot.com/2022/03/babbar-kotun-tarayya-ta-bayar-da.html Malami dai ya tabbatar da cewa, zai yi ma dokar gyaran fuska. Tun da farko dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa dokar hannu tare da rokon 'yan majalisar dattawan Najeriya da su yi ma ta kwaskwarima wajen cire wannan sashe, amma suka ki amincewa da wannan bukata. Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan kafin gudanar da babban zaben jam'iyyar APC da zai gudana a ranar 26 ga wannan wata na Maris. Kuma a na ganin zai iya kara haifar da baraka cikin jam'iyyar.

Babbar Kotun Tarayya Ta Bayar Da Umurnin Soke Sashe na 84 Da Ya Hana Masu Rike Da Mukaman Siyasa Tsayawa Takara

Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Umuahia, Jihar Abia, ta umurci Babban Lauyan Tarayya da ya gaggauta soke sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.  Yayin da yake rattaba hannu a kan kudirin dokar zabe a watan da ya gabata, shugaba Buhari ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta soke sashe na 84 (12), wanda ya haramta wa mambobin majalisar zartaswa tsayawa takara ba tare da yin murabus ba. Shugaban ya kara da cewa, “Sashe na 84 (12) ya kunshi hana masu rike da mukaman siyasa damar kada kuri’a ko zabe a babban taro ko na kowace jam’iyya, domin gabatar da ‘yan takara a kowane zabe.  Sai dai Majalisar Dattawa ta ki yin la’akari da bukatar shugaban kasar, inda ta yi watsi da kudirin dokar da ke neman a yi wa sashen kwaskwarima, inda ‘yan majalisar suka jaddada cewa gyaran sashe na 84 (12) zai saba wa ma’aikatan gwamnati.  

Illolin Amfani Da Rikitacciyar Jimla A Rubutu Ko Rediyo

Papertrue.blog *" A kokarin hada su da 'yan'uwansu da sanadiyyar rikice-rikice suka rabu ." A yadda harshe ya ke da wuyar sha'ani wajen aikewa da sako, wajibi ne a kaucewa kowace irin jimla mai harshen damo ko mai iya haddasa rudani a kwalkwalwar mai karatu ko saurare. A maimakon haka ya fi dacewa a ce, " A kokarin hada su da 'yan'uwansu da tashe-tashen hankula suka raba" Dalili kuwa kalamar rikici ba ta dace da nan ba saboda ko mutum biyu na iya rikici da juna.  Rikici na nufin jayayya ko rashin yarda da abu da zai iya haifar da rashin matsaya daya, wanda kuma zai kai ga fada. Mutane na iya yin gaba da juna akan rikici na siyasa ko gado. Amma ita kalmar tashin hankali a bayyane ta ke ga mai saurare, sakamakon irin yadda kalmar ta zama tamkar ta yi kaka-gida saboda yadda yankunan arewacin Najeriya ke fama da tashe-tashen hankula. Me Ya Kawo Rudani A Nan? A jimla ta farko mai saurare zai dauka rikicin tsakanin 'yan'uwan ya ke, ...

Bambancin Bayar Da Labari A Rediyo Da Kuma Talabijin

Shi mai gabatar da shiri a rediyo kullum ya sani sauraren sa ake yi, ba kamar yadda ake kallo a talabijin ba, kan haka dole ya yi amfani da  descriptive words, wato kalmomi masu hoto ,  domin mai saurare ya ga hoton abin a kwakwalwarsa, har ma ya ji dadi a ransa. Getty images Ya Misalin Haka Ya Ke Ga Mai Saurare? Mai saurare na bukatar ganin zahirin hoton abinda mai bayar da labari ke fada. Kunnuwa ke sauraren labarin amma kwakwalwa za ta ci gaba da sarrafa hoton abinda ake siffatantawa. Misalain haka shi ne a suranta maka gida ta hanyar zayyano dukan abinda ya mallaka, kamar kofofi biyu hannun riga da juna da farin fenti sai tagogin gilashi ma su karau-karau ga kuma furanni da aka kawata harabarsa farare da jajaye da kuma rawaya. Nan ta ke kwakwalwar mai saurare za ta dauki hoton har yadda za ku iya ganin sa. Ga Misalin Haka: "Gaba daya kankara ta mamaye tsaunukan sun yi fari fat tamkar auduga. A duk shekara irin wannan lokcin sanyi, ruwan gulabe ...

Ranar Bacci Ta Duniya Ta Zagayo

Kowace rana ta Allah na da nata amfani: aiki da karatu da ibada. Majalisar Dunkin Duniya ta kebe kowace rana kamar yadda yau ta zama ranar bacci ta duniya. Shin ko kun san bacci na kara lafiyar kwakwalwa da taimaka ma mai karatu, kuma wadanne lokuta kuka fi jin dadin bacci?

Buhari Ya Ce Maimala Ne Shugaban APC

A wani abu da ake ganin kamar zai iya haddasa sabuwar baraka a cikin jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci gwamnonin APC su bar gwamnan jahar Yobe Maimala Buni ya dore kan shugabancin jam'iyyar. Gwamnan dai ya isa birnin Landan tare da rakiyar Ministan ilmi Malam Adamu Adamu, in da kuma ya gana da shugaban kasar. A farkon makon jiya dai ne wasu jiga-jigan jam'iyyar APC suka maye gurbinsa da gwamnan jahar Naija Abubakar Sani Bello, wanda nan take ya rantsar shugabannin kwamitin gudanane da babban zaben jam'iyyar na kasa da ane sa ran yi a ranar 26 ga wannan wata na Maris. An jiyo gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufa'i a wata hira da tashar talabijin ta Channels na cewa, gwamnan jahar Naija ne ya samu sahakewar shugaban kasa. El-Rufa'i ya ce, sun kafa wani kwamiti da suka tuntubi shugaban kasar, in da kuma ya amince da Sani Bello a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar APC na kasa. A ganin masana, wasu na amfani da sunan shugaba...

Shugaban Rasha Ya Nunawa Biden Yatsa

ewn.co.za Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce kalaman da shugaban Amurka Joe Biden ya yi ba za su tafi a banza ba. Yana dai mayar da martani ne akan kalaman shugaba Amurka da ya ce, "Putin azzalumi ne kuma wanda ya aikata manyan laifukan yaki". Sai dai shugaba Putin ya ce ba za ta taba yuwa Rasha ta yafe ma Amurka ta kowane fanni ba sakamakon wadannan kalamai da ya kira, "na cin zarafin kasarsa". Yanzu haka dai yakin da kasashen Ukraine da Rasha ke ci gaba da gwabzawa ya shiga mako na uku in da munana hare-haren da dakarun Rasha ke kaiwa suka yi sanadiyyar hallakar fararen hula da dama, ciki kuwa har da yara kanana. npr.org Kasashen da ke karkashin kungiyar tsaro ta NATO sun zakuda gefe guda ba tare da amincewa su tsunduma cikin yakin ba, in da suka bayar da hujjar cewa tsunduma yakin na iya haifar da yakin duniya na uku. Sai dai a maimakon haka sun tsananta sakawa Rasha karin takunkumai da suka hada da kin sayen man da ta ke hakowa, da...

Kalubalen Fassarar Labarai A Rediyo

Fassara dai na nufin juya ma'ana daga wani harshe zuwa wani ba tare da canza sakon asali ba. Ya zama wajibi mai fassara ya zama mutum mai cikakken hankali, da ya mallaki harsunan da yake fassara daga gare su zuwa gare su. Abin da ake nufi a nan shi ne cewa dole ne mai yin fassara ya san harsunan da zai yi wa fassara, sannan ya yi musu kyakkyawar fahimta; wato ya san harshen da aka yi magana da shi, sannan da wanda zai juya maganar zuwa cikinsa. Misali, wanda zai riÆ™a yin fassara daga Ingilishi zuwa Hausa dole ya fahimci harshen Hausar da kuma Ingilishi, fahimta kuma ta haÆ™iÆ™a. Sanin al’adu: Dole ne mai yin fassara ya san al’adun waÉ—anda zai fassara maganar zuwa harshensu. Misali, idan mai fassara zai yi fassara zuwa harshen Hausa, to dole ya san al’adun Hausawa, sani kuma ba na shanu ba. Haka kuma, dole ne mai yin fassara ya kasance mai zurfafa bincike a fannonin ilimi dan ya samu isassun kalmomin da za su taimaka masa wajen yin kyakkyawar fassara. Amma idan bai fahimci...

Karancin Man Fetur Ya Mayar Da Tituna Fayau

Yau an wayi gari da dogayen layuka a gidajen mai na jahar Sokoto sakamakon tsananin karancin man fetur da ake fama da shi a Najeriya fiye da wata biyu. Galibin hanyoyin mota sun zama kusan fayau sabanin yadda aka saba, yayinda dimbin direbobi suka mamaye ciki da harabar gidajen man jahar.  Tantabara News ta samu zantawa da wasu da ke kokarin samun man da suka bayyana cewa abin ya wuce hankali. Wani direba mai suna Umar Dogon Daji ya ce, " a watannin baya muna sayen litar mai naira 165, amma yanzu akwai in da ya kai har 260". Duk da irin wannan yanayi babu wata alamar kawo karshen wannan matsala da ta addabi kasar nan tsawon shekaru. Wani dan bunmburutu ya sanar da wakilinmu irin yadda su ma suke shan wahala kafin su samu nasarar sayen mai a kasuwar bayan fage. Mutumin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, " mu ma 'yan bunmburutu muna shan wuya kwarai da gaske, sai ma mun bayar da toshiyar baki sannan a ke zuba muna man". Ya kara...

Hukumar Hana Fasa Kwabri Ta Najeriya Ta Kama Buhunan Naman Jaki 1,339

Hukumar ta bayyana kama wannan adadin buhunan naman jaki ne a jahar Kabi da ke arewa maso yammacin Najeriya da aka kiyasta kudinsu ya haura naira miliyan 40. Shuguban hukumar ta kastam Joseph Attah ya ce sun yi nasarar kama kyafaffen naman jakin ne da aka shirya fita da shi. A cewar sa wadanda aka kama da naman sun bayyanawa hukumar cewa fiye da jakuna dubu daya suka yanka kafin su tara wannan adadi. Gwamnatin Najeriya dai ta haramta safarar jakuna zuwa kasashen ketare musamman kasar Sin, wadda ke sahun gaba wajen sayen jakuna a kasashen Afirka da suka hada da Najeriya da Nijar da Mali da Sudan da sauran su. A halin da ake ciki yanzu haka jakuna na barazanar karewa a duniya sakamakon yawan safarar su da ake tare da sarrafa nama da fatarsu ta wasu hanyoyi na daban. Hasalima dai, jaki dabba ce da kan hai fi da daya kwal a cikin shekaru ba kamar sauran dabbobi ba da ke haihuwa biyu zuwa uku a shekara.

NDE Has Begun Training 50 People on Entrepreneurship and Financial Counselling in Sokoto

National Directorate of Employment (NDE) has begun training 50 people on entrepreneurship and financial counselling in Sokoto on Monday 7th March, 2022, to enable them contribute to national development. Director-General of NDE, Mr Abubakar Nuhu Fikpo, represented by the Sokoto State Coordinator, Mrs Eunice J. Danmallam, said this at the opening of the five-day training held at Shamsuddeen Plaza Sokoto. According to her the training would enable unemployed graduates of tertiary institutions to become self-reliant through the vehicle of entrepreneurship. She said that the goal of the training was to unleash the potentials of the participants and they will be sensitized on the realities of the Nigerian labour market and trained on the types of businesses that fit their interests, skills and competencies. Beneficiaries will be trained on how to write viable feasibility studies with which to source for funds to expand or establish their businesses. Howev...

Who Do Vladimir Putin Consult Before Making a Decision?

Reuters In recent weeks, Russian President Vladimir Putin has taken a number of important steps that will not only affect Ukraine and Russia, but also the rest of the world. Who did he consult while making that decision?  What is the reason for this military action - or the influence of the siloviki group of powerful security chiefs and ministers? It can be said that Russia is a country whose leaders are very powerful. President Vladimir Putin holds the reins of power in the country, and he himself decides all matters affecting the country. However, he is in contact with the National Security Council, especially those he has known and trusted for a long time. There are some well-known security agencies in Russia called siloviki .  Vladimir Putin himself began working in such security agencies like the KGB, and even became the Russian Federal Security Service or FSB. The Slovak group has been gaining momentum since Putin came to power. Five Main Things Important sec...