Skip to main content

An Hana Masu Mukaman Siyasa Jefa Kuri'a A Babban Taron APC Na Kasa

Kwamitin tsare-tsare na musamman na riko na jam’iyyar APC ya kori masu rike da mukaman siyasa daga kada kuri’a a babban taron kasa na ranar Asabar.

A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana karara cewa “dukkan wadanda aka nada a siyasance da aka zaba a matsayin wakilai a babban taron kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 26/3/2022, ba za su kada kuri’a ba bisa la’akari da cece-kucen da ke tattare da sashe na 84 (12) na dokar zabe.  2022."


Komitin, duk da haka, ya bayyana cewa masu nadin siyasa na iya halarta a matsayin masu sa ido kawai amma kada su dada kada su rage.

Hakan ya biyo bayan amincewar da Majalisar Dokoki ta kasa baki daya ta yi da dokar gyaran dokar zabe da shugaban kasa Muhammadu ya sanya wa hannu

Alamu sun bayyana a ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa da gwamnonin jam’iyyar APC suka amince da batun fitowar jami’an jam’iyyar, ciki har da shugaban jam’iyyar na kasa.

A jiya alhamis shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin APC in da suka daddale matsaya tare da gindaya nasu sharudda da kuma shugaban kasar ya amince da su
Wannan ya nuna kusan jam'iyyar ta dunke barakar da ke son kunno kai cikin ta ana sauran kwana daya ta gudanar da babban taronta na kasa da zai haska makomar jam'iyyar nan gaba.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey