Skip to main content

Kwankwaso Ya Fice Daga PDP

Getty images
Labarin da ke shigo muna yanzu haka sun tabbatar da tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fitar da sanarwar ficewa daga jam'iyyar ta PDP zuwa sabuwar jam'iyyar NNPP, jim kadan bayan da kotu ta bayar da umurnin dakatar da helkwatar jam'iyyar PDP ta kasa daga rusa membobin kwamitin zartaswar jam'iyyar reshen jahar Kano.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

An Sako Ƙarin Fasinjojin Jirgin Ƙasa Bakwai Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na ranar 28 ga Maris a jihar Kaduna sun samu 'yanci. An sako mutanen ne a safiyar Laraba bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan. Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga 'yan ta'addar domin a sako su ba. Ɗaya daga waɗanda suka shiga sasantawar mai suna Tukur Mamu, ya fada  a wata sanarwa a ranar Laraba cewa shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu.  Sanarwar ta ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani