Skip to main content

Posts

Gwamnatin Tarayya Ta Shawarci ÆŠalibbai Su Maka ASUU Kotu

Kasancewar zaman tattauna tsakanin Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) da gwamnatin tarayya an tashi dutse a hannun riga, hakan ya fusata gwamnatin tarayyar Najeriya, in da aka jiyo Ministan Ilmin ƙasar, Malam Adamu Adamu na shawartar ɗaliban jami'ar da ke zaman jira a gida na su maka ƙungiyar a kotu. Ministan ya ce dukan alhakin ɓatawa ɗaliban lokaci ya rataye a wuyan malaman jami'a, kuma ya zama wajibi su biya ɗaliban diyya. Ya kuma ce gwamnatin tarayya za ta saka ƙafar wando guda da malaman ta hanyar ƙin biyansu albashin watannin da suka kwashe ba tare da aiki ba. Wasu daga cikin malaman jami'ar sun fara mayar da martani kan wannan matsaya ta gwamnatin tarayya. Dakta Mansur Isah Buhar, na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, "Na amice ɗari bisa ɗari cewa adalci ne kada a biya membobin ASUU albashinsu na tsawo wata shida da suka kwashe suna yajin aiki, saboda kuwa ai ba su yi aikin da ya dace a ce sun y...

Hukumar Lura Da Kafafe Watsa Labarai Ta Najeriya Ta Ƙwace Lasisin Gidajen Rediyo Da Talabijin 52

Shugaban hukumar ta NBC Malam Balarabe Shehu Illela ne ya sanar da hakan a yau jumu’a, in da ya bayyana cewa akwai É—imbin bashin da ya kai naira biliya 2 da rara da ake biyar gidajen talabijin na African Independent Television (AIT) da Silver Bird Television da aka fi sani da (STV) tare da Æ™arin wasu 52. Shugaban hukumar ya ce dokar Najeriya mai Lamba CAP N11, Sashe na 10, ta shekarar 2004 ta ba hukumar NBC wannan dama, kuma tun a watan Mayun bana ne suka wallafa sunayen kafafe watsa labaran da suka kasa sabunta lasisinsu tare da umurtar su da yin haka a cikin mako biyu rak, ko su fuskanci wannan mataki na karÉ“e mu su lasisi. Wannan matakin dai ana ganin shi ne irin sa na farko a tarihin Najeriya da ya shafi gidajen rediyo mallakar jahohi da masu zaman kansu. Kazalika, masana na fassara shi da wani salon gwamnatin tarayya na yaÆ™ar ‘yancin faÉ—ar albarkacin baki. Wasu daga gidajen rediyo da wannan dakatarwar ta shafa sun haÉ—a da Gidan Rediyon Rima na Sokoto da Rediyon Jahar K...

Salman Rushdie Na Cikin Mawuyacin Hali

Tun  bayan da wani matashi a birnin New York na Amurka, mai suna Hadi Matar ya sokawa marubucin wuÆ™a ya ke kwance a wani asibiti a birnin. A jiya lahadi aka gurfanar da mista Mata a gaban wata kotu in da ya musanta laifukan yunÆ™urin kisan kai da ake zargin sa da yi. AlÆ™alin kotun Jason Schmidt ya bayar da umurnin ci gaba da tsare shi ba tare da bayar da beli ba har zuwa lokacin da za a sake gabatar da shi a gaban kotun. Wani makusancin Salman Rushdie mai suna Andrew Wylie, ya sanar da cewa  Mista Rushdie na cikin halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai sakamakon munanan raunukan da ya samu bayan da aka daÉ“a ma sa wuÆ™a a fuska da wuya da kuma cikinsa, abinda ya kai ga taÉ“a hantarsa. Kusan shekara 10 kenan Salman Rushdie na famar É“uya, tun daga lokacin da shugaban addinin Æ™asar Iran, Ayatullahi Ruhullah, ya bayar da umurnin a kashe shi tare da saka ladar dala miliyan 3 ga duk wanda ya kashe shi. Sannan a shekarar 2012 gwamnatin ta Farisa ta Æ™ara wasu dala 500,000 bisa ga na f...

'Yan Jarida Na Shan ÆŠauri A Rasha

Wata ‘yar jaridar wani gidan talabijin na Rasha, Marina Ovsynnikova, ta fuskanci É—aurin wata biyu saboda ta bayyana rashin goyon baya akan mamayar da Æ™asarta ke ci gaba da yi wa Yukren. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, wata kotu ta sanar da kama Ovsynnikova da laifin cin amanar Æ™asa, sakamakon É—aga kwalin da ta yi a kusa da fadar Kremlin mai É—auke da kalaman da ke cewa, “Putin mai kisan kai ne, yara nawa suka mutu sakamakon aikinka, ka gaggauta dakatar da wannan yaÆ™i”. Gwamnatin Rasha ta daÉ—e tana É—aure masu adawa da mamayar da ta ke yi ma Yukren, tare da bayyana yaÆ™in  da sunan “aikin dakarun soji na musamman” kuma shugaba Putin ya sha alwashin tsare duk waÉ—anda aka samu da laifin watsa labarun Æ™arya  tsawon shekara goma a gidan jarum.

Cire Iyorchia Ayu Daga Shugaban Jam’iyyar PDP Kasada Ce – Debo Ologunagba

A wani zaman sulhu da ake ci gaba da yi a Abuja, gwamnan jahar Rivers Nyesom Wike da tsohon mataimakain jam’iyar PDP na yankin kudu, Chif Olabode George, na cikin sahun gaba wajen ganin jam’iyar ta cire shugabanta na yanzu, Iyochia Ayu daga muÆ™aminsa muddin a na neman zaman sulhun ya kai ga haifar da É—a mai ido. A cewar su, hakan ne kawai zai iya samar da daidaito ga yankin kudancin Najeriya kasancewar ba adalci ne ba É—an takarar shugaban Æ™asa da shugaban jam’iya su fito a yanki guda ba. To, amma kuma wannan buÆ™ata ta gamu da cikas in da a yayin hirarsa da manema labarai a Abuja, Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce ba za ta saÉ“u ba, domin cire shi kasada ce, da za ta iya jefa PDP cikin sabon ruÉ—ani.  Ya Æ™ara da cewa, “ai a fili take Æ™arara, kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanadar duk lokacin da aka cire shugaban jam’iyya a bisa kowane dalili ne kuwa, to mataimakinsa kan maye gurbinsa kuma ya zama sun fito daga shiya É—aya. Kazalika, kundin tsarin m...

An Sako Ƙarin Fasinjojin Jirgin Ƙasa Bakwai Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na ranar 28 ga Maris a jihar Kaduna sun samu 'yanci. An sako mutanen ne a safiyar Laraba bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan. Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga 'yan ta'addar domin a sako su ba. ÆŠaya daga waÉ—anda suka shiga sasantawar mai suna Tukur Mamu, ya fada  a wata sanarwa a ranar Laraba cewa shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu.  Sanarwar ta ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani

Jami’an Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI Sun Kai Samame Gidan Dold Trump

  Tsohon shugaban Æ™asar Amurka Donald Trump ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa tawagar jami’an hukumar sun mamaye gidansa na alfarma da aka fi sani da suna Ma-a-Lago da ke a gaÉ“ar tekun jahar Fulorida. Rahotanni sun nunar da cewa samamen na da nasaba da wani bincike da ake kan gudanarwa da ke zargin Mista Trump da riÆ™e wasu muhimman takardun gwamanati tun bayan saukar sa daga mulki. Sai dai Mista Trump ya bayyana wannan mataki da kutsen da ya saÉ“awa doka, “Babu wani abu makamancin wannan da ya taÉ“a faruwa da Shugaban Amurka a tarihance”. Sashen adana bayanan gwamnatin Amurka ya sanar tun a farko cewa, Mista Trump bai miÆ™a wasu muhimman takardu ba da suka haÉ—a da wasiÆ™u da ya zama wajibi duk shugaban Æ™asa mai barin gado ya hannunta bayan barin sa mulki. Jami’an ofishin sun ce sun gano manyan akwatuna 15 a gidan waÉ—anda ke É—auke da muhimman takardun. Daga baya sashen adana bayanan ya shaidawa majalisar dokokin Amurka cewa kowace akwati da aka gano an yi mata a...

Gwamna Tambuwal Ya Umurci Malaman Jami'ar Sokoto Su Koma Aiki

Gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya umurci Malaman Jami’ar  Jahar Sokoto da su koma bakin aiki ba da bata lokaci ba,bayan kwashe wata shida jami’ar na rufe  sakamakon yajin aikin Kungiyar Malamn Jami’a (ASUU). Wannan mataki na kama da bayar da umurnin nan take in da ya nuna matukar bacin ransa yadda malaman ke ci gaba da kauracewa wuraren aikinsu da zimmar bin umurnin kungiyar ta ASUU. Ya kuma nunar da cewa babu wani hakki da malaman jami’ar Jahar Sokoto ke bin gwamnatinsa kama daga albashi ya zuwa sauran bukatu da bai yi mu su ba. Ya bayyana cewa babu wata matsala a duniya da ta gagari tattaunawar da za ta kai ga cimma maslaha, kuma ya zama wajibi a fito da matakin da zai iya zama kandagarki ga duk wani abu da ke haifar da yajin aiki a Najeriya. “Bai kamata ku biyewa uwar kungiya ta ASUU ba, saboda matsalolinsu ba su shafe ku ba. Kuna cutar da dalibanku ne kawai, kuma wannan biyayyar da kuke  ci gaba da yi na da matukar muni da nakasu ga makomar i...

Kalubalen Tsaro Da Canza Shekar Kwamishinan Tsaron Jahar Sokoto

  A daidai lokacin da matsalar tsaro ke Æ™ ara ta’azzara a jahar Sokoto, kwamishinan tsaron jahar Kanal Garba Moyi (mai ritaya) ya bayar da sanarwar aje mu Æ™ aminsa tare da ficewa daga jam’iyyar jam’iyar PDP mai mulkin jahar. A cewar tsohon kwamishinan tsaron, “akwai gaggan matsaloli da suka taka rawa wajen ficewarsa daga jam’iyayar, da suka ha É— a da sakacin gwamnan jahar, Aminu Waziri Tambuwal na watsi da dukan   shawarwarin da ake ba shi da suka shafi tsaro; kazalika da rashin sauraren Æ™ orafe- Æ™ orafen dangane da ci gaban jahar a fannoni da dama”. A ranar alhamis da ta gabata dai wasu ‘yan bindiga suka kai wani hari a garin Chakai da ke Ƙ aramar Hukumar Mulki ta Tambuwal, wadda ita ce mahaifar gwamnan jahar, in da suka sace mutum goma sha bakwai ciki har da mata da Æ™ ananan yara, tare da neman diyyar naira miliyan takwas da dubu É— ari biyar. Kazalika, sun fitar da sanarwar shirin hallaka mutanen daga gobe talata, muddin ‘yan uwan wadanda ake garkuwa da sun ba su aika...

INEC Ta Yi Watsi Da Lawan Ta Tabbatar Da Machina

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta Najeriya (INEC) ta fitar da sabuwar sanarwa a jiya alhamis 23 ga watan Yuni, 2022 da ke tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin halastaccen dan takarar kujerar dan majalisar dattijai na kasa mai wakiltar kananan hukumomin Machina da Gashuwa da Nguru da Jakusko da Yusufari da Bade da kuma Karasuwa jahar Yobe, in da kuma ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa ba ta san da wani zaben fidda gwani da aka gudanar ba koma bayan wanda ya wakana a ranar 28 ga watam Mayu. A cewar INEC babu wani dan takara da ta sani face Bashir Sheriff Machina. Tun da farko dai Sanata Ahmad Lawan ne ke wakiltar wadannan kananan hukumomin, wanda hukumar ta bayyana da cewa ya nemi mukamin shugaban kasa a maimakon matsayin da ya ke akai yanzu haka na dan majalisar dattijai. An dai jiyo shugaban jami'iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu, a wata hira da sashen Hausa na BBC na bayyana cewa ba su san da wani ba sai sanata Ahmed Lawan, abinda ya jawo cece-ku-ce....