Skip to main content

Posts

Jam'iyyu 13 Sun Yi Barazanar Ƙauracewa Zaɓe A Najeriya

Gamayyar jam'iyyun adawa 13 sun bayyana cewa za su ƙauracewa shiga zaɓe muddin Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙara wa'adin amfani da tsofaffin kuɗaɗe daga lokacin da aka ɗiba tun da farko. Shugaban jam'iyyar AA Kennetth Udeze ne ya fitar da wannan sanarwa, in da ya ce canjin fasalin kuɗi da CBN ya fito da shi zai haifar da babban tasiri a tattalin arziki da fannin tsaro kana sun kai matsayar watsi da sabon matakin da gwamnonin APC suka ɗauka da suka haɗa da na Kaduna, Malam Nasiru El-rufai da na Zamfara Bello Mutawalle da na Kogi Yahaya Bello, na maka shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gaban kotu kan sauya takardun kuɗi da ya yi. A Najeriya akwai jerin jam'iyyu 18 da za su fafata a babban zaɓe mai zuwa sai dai 13 daga ciki sun yi barazanar janye jikinsu daga shiga zaɓen muddin aka ƙara lokacin amfani da tsofaffin kuɗaɗe. Menene ra'ayinka kan wannan batu?

Yadda Masu Kuɗi Da Ruwa Suka Cika Harabar ATM

Rahotonni da ke ci gaba da shigo muna yanzu haka, na nuni da cewa ɗaruruwan mutane na ta yi dogayen  layuka a gaban na'urar cirar kuɗi ta ATM da ke bankuna, inda suke amfani da wani salo na biyan mutane domin su ciro mu su kuɗi. Wani da muka zanta da shi mai suna Lawal Mai Masara, ya shaida muna cewa, tun jiya ya ke kan layi, kuma har yanzu bai kai ga samun kuɗin ba saboda masu sana'ar POS da masu kwashe kuɗi su sake adanawa sun cika ko'ina. "Za ka ga mutane riƙe da katunan cirar kuɗi fiye da 10 inda suke tura ma wasu kuɗi su rarraba musu katunan domin a cire mu su kuɗin a ATM daga baya su bayar da naira dubu akan duk dubu goma da aka cire mu su". In ji shi. Mutumin ya ƙara da cewa wannan na daga cikin manyan dalilan da suka haddasa ƙarancin kuɗi tsakanin mutane a Najeriya.musamman arewa. Wannan sabon matakin ya nuna irin yadda mutane ke jefa kansu a halin tasku ta hanyar ci gaba da kwashe kuɗaɗen da jama'a ya kamata su samu. Wani ganau...

Wike Ya Tona Magoya Bayan Atiku A Fadar Shugaban Ƙasa

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun tabbatar masa da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar da magoya bayansa, na taƙama da cewa ba sa buƙatar goyon bayan gwamnonin G5 kafin su ci nasara zaɓe, saboda wasu tsiraru a fadar shugaban ƙasa sun ba su tabbacin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. Jaridar POLITICS NIGERIA  ta ruwaito cewa gwamnan yayi magana ne a garin Ibaka a yayin gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas na ƙaramar hukumar Okrika a ranar Juma’a. "Na ce an ba su tabbaci, amma wannan zaɓen ba zai dogara ne akan wannan tabbacin ba, yana kan tabbacin mutane ne,” in ji Wike. Gwamna Wike dai ya dage cewa har yanzu Atiku na buƙatar jihar Ribas don samun nasara ko kuma ya faɗi zaɓe a 2023. A cewarsa, “ko kuna so ko ba ku so, dole ne ku buƙaci jihar Ribas. Idan ba ku buƙatar Jihar Ribas to dole ne ku sha ƙasa. Idan kun ce ba ku son mu, lallai kuwa za ku gaz...

Canjin Kuɗi Alfanu Ne - Peter Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour Party Mista Peter Obi, ya shawarcin 'yan Najeriya da su rungumi sabon tsarin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito da shi na canjin fasalin kuɗi, in da ya ce yana da muhimmanci. Ya roƙi 'yan Najeriya da su marawa tsarin baya, wanda a cewar sa  ba Najeriya ce ta farko a canza fasalin kuɗi ba a duniya, sai dai wannan ya zo da wahala ga jama'a amma kuma yana da matuƙar amfani ga tattalin arzikin ƙasa  da walwalar jama'a duk da akwai buƙatar a inganta shi. Mista Obi ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a ƙarshen makon nan. Peter Obi dai ya taɓa zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar a 2019 kafin yanzu shi ma ya fito neman wannan kujera a babban zaɓe mai zuwa.

INEC Ta Yaba Yadda Na'urar BVAS Ke Aiki

Shugaban Hukumar Zaɓe INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa gwajin da aka yi na tantance masu jefa kuri'a ya nuna na'urar BVAS da aka fito da ita na yin aiki yadda ya dace. Shugaban hukumar ya bayyana hakan yayin da ya ke ganawa da manema labarai a birnin Tarayya Abuja. Ya ce "naurar na iya tantance masu zaɓe cikin dakika 30 kuma babu wata alamar tasgaro a tattare da ita". Farfesa Yakubu ya ce sun tanadi na'urorin wucin gadi ko da aka yi wasu daga cikin na'urorin su kasa lokacin da ake tantance mazu jefa kuri'a da su. 

President Buhari Opens The Nigerian Chief of Army Staff Annual Conference 2022 in Sokoto

President Muhammadu Buhari  declared open the Nigerian Army Chief of Army Staff Annual Conference 2022 in Sokoto. The conference tagged: “Building a Professional Nigerian Army for the 21st Century Security Environment” was commenced at the multipurpose Hall of the International Conference Center Kasarawa, in Sokoto State. President Buhari said Nigerian Army has over the years demonstrated its capacity and zeal in defending Nigeria’s territorial integrity and sovereignty against external aggression and giving aid to civil authority in mitigating internal security challenges in the country. He explained that under his administration from 2015 to date, the Nigerian Army has achived a significant success in fighting against insergency particularly in the Nirth East and North West. He maintained that the troops’ giant strides have led to the mass surrendering of terrorists and their family members in droves. Troops have also maintained this feat, through their operational en...

Gwamnatin Tarayya Ta Shawarci Ɗalibbai Su Maka ASUU Kotu

Kasancewar zaman tattauna tsakanin Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) da gwamnatin tarayya an tashi dutse a hannun riga, hakan ya fusata gwamnatin tarayyar Najeriya, in da aka jiyo Ministan Ilmin ƙasar, Malam Adamu Adamu na shawartar ɗaliban jami'ar da ke zaman jira a gida na su maka ƙungiyar a kotu. Ministan ya ce dukan alhakin ɓatawa ɗaliban lokaci ya rataye a wuyan malaman jami'a, kuma ya zama wajibi su biya ɗaliban diyya. Ya kuma ce gwamnatin tarayya za ta saka ƙafar wando guda da malaman ta hanyar ƙin biyansu albashin watannin da suka kwashe ba tare da aiki ba. Wasu daga cikin malaman jami'ar sun fara mayar da martani kan wannan matsaya ta gwamnatin tarayya. Dakta Mansur Isah Buhar, na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, "Na amice ɗari bisa ɗari cewa adalci ne kada a biya membobin ASUU albashinsu na tsawo wata shida da suka kwashe suna yajin aiki, saboda kuwa ai ba su yi aikin da ya dace a ce sun y...

Hukumar Lura Da Kafafe Watsa Labarai Ta Najeriya Ta Ƙwace Lasisin Gidajen Rediyo Da Talabijin 52

Shugaban hukumar ta NBC Malam Balarabe Shehu Illela ne ya sanar da hakan a yau jumu’a, in da ya bayyana cewa akwai ɗimbin bashin da ya kai naira biliya 2 da rara da ake biyar gidajen talabijin na African Independent Television (AIT) da Silver Bird Television da aka fi sani da (STV) tare da ƙarin wasu 52. Shugaban hukumar ya ce dokar Najeriya mai Lamba CAP N11, Sashe na 10, ta shekarar 2004 ta ba hukumar NBC wannan dama, kuma tun a watan Mayun bana ne suka wallafa sunayen kafafe watsa labaran da suka kasa sabunta lasisinsu tare da umurtar su da yin haka a cikin mako biyu rak, ko su fuskanci wannan mataki na karɓe mu su lasisi. Wannan matakin dai ana ganin shi ne irin sa na farko a tarihin Najeriya da ya shafi gidajen rediyo mallakar jahohi da masu zaman kansu. Kazalika, masana na fassara shi da wani salon gwamnatin tarayya na yaƙar ‘yancin faɗar albarkacin baki. Wasu daga gidajen rediyo da wannan dakatarwar ta shafa sun haɗa da Gidan Rediyon Rima na Sokoto da Rediyon Jahar K...

Salman Rushdie Na Cikin Mawuyacin Hali

Tun  bayan da wani matashi a birnin New York na Amurka, mai suna Hadi Matar ya sokawa marubucin wuƙa ya ke kwance a wani asibiti a birnin. A jiya lahadi aka gurfanar da mista Mata a gaban wata kotu in da ya musanta laifukan yunƙurin kisan kai da ake zargin sa da yi. Alƙalin kotun Jason Schmidt ya bayar da umurnin ci gaba da tsare shi ba tare da bayar da beli ba har zuwa lokacin da za a sake gabatar da shi a gaban kotun. Wani makusancin Salman Rushdie mai suna Andrew Wylie, ya sanar da cewa  Mista Rushdie na cikin halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai sakamakon munanan raunukan da ya samu bayan da aka daɓa ma sa wuƙa a fuska da wuya da kuma cikinsa, abinda ya kai ga taɓa hantarsa. Kusan shekara 10 kenan Salman Rushdie na famar ɓuya, tun daga lokacin da shugaban addinin ƙasar Iran, Ayatullahi Ruhullah, ya bayar da umurnin a kashe shi tare da saka ladar dala miliyan 3 ga duk wanda ya kashe shi. Sannan a shekarar 2012 gwamnatin ta Farisa ta ƙara wasu dala 500,000 bisa ga na f...

'Yan Jarida Na Shan Ɗauri A Rasha

Wata ‘yar jaridar wani gidan talabijin na Rasha, Marina Ovsynnikova, ta fuskanci ɗaurin wata biyu saboda ta bayyana rashin goyon baya akan mamayar da ƙasarta ke ci gaba da yi wa Yukren. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, wata kotu ta sanar da kama Ovsynnikova da laifin cin amanar ƙasa, sakamakon ɗaga kwalin da ta yi a kusa da fadar Kremlin mai ɗauke da kalaman da ke cewa, “Putin mai kisan kai ne, yara nawa suka mutu sakamakon aikinka, ka gaggauta dakatar da wannan yaƙi”. Gwamnatin Rasha ta daɗe tana ɗaure masu adawa da mamayar da ta ke yi ma Yukren, tare da bayyana yaƙin  da sunan “aikin dakarun soji na musamman” kuma shugaba Putin ya sha alwashin tsare duk waɗanda aka samu da laifin watsa labarun ƙarya  tsawon shekara goma a gidan jarum.