Skip to main content

Posts

An Sako Ƙarin Fasinjojin Jirgin Ƙasa Bakwai Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na ranar 28 ga Maris a jihar Kaduna sun samu 'yanci. An sako mutanen ne a safiyar Laraba bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan. Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga 'yan ta'addar domin a sako su ba. ÆŠaya daga waÉ—anda suka shiga sasantawar mai suna Tukur Mamu, ya fada  a wata sanarwa a ranar Laraba cewa shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu.  Sanarwar ta ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani

Jami’an Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI Sun Kai Samame Gidan Dold Trump

  Tsohon shugaban Æ™asar Amurka Donald Trump ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa tawagar jami’an hukumar sun mamaye gidansa na alfarma da aka fi sani da suna Ma-a-Lago da ke a gaÉ“ar tekun jahar Fulorida. Rahotanni sun nunar da cewa samamen na da nasaba da wani bincike da ake kan gudanarwa da ke zargin Mista Trump da riÆ™e wasu muhimman takardun gwamanati tun bayan saukar sa daga mulki. Sai dai Mista Trump ya bayyana wannan mataki da kutsen da ya saÉ“awa doka, “Babu wani abu makamancin wannan da ya taÉ“a faruwa da Shugaban Amurka a tarihance”. Sashen adana bayanan gwamnatin Amurka ya sanar tun a farko cewa, Mista Trump bai miÆ™a wasu muhimman takardu ba da suka haÉ—a da wasiÆ™u da ya zama wajibi duk shugaban Æ™asa mai barin gado ya hannunta bayan barin sa mulki. Jami’an ofishin sun ce sun gano manyan akwatuna 15 a gidan waÉ—anda ke É—auke da muhimman takardun. Daga baya sashen adana bayanan ya shaidawa majalisar dokokin Amurka cewa kowace akwati da aka gano an yi mata a...

Gwamna Tambuwal Ya Umurci Malaman Jami'ar Sokoto Su Koma Aiki

Gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya umurci Malaman Jami’ar  Jahar Sokoto da su koma bakin aiki ba da bata lokaci ba,bayan kwashe wata shida jami’ar na rufe  sakamakon yajin aikin Kungiyar Malamn Jami’a (ASUU). Wannan mataki na kama da bayar da umurnin nan take in da ya nuna matukar bacin ransa yadda malaman ke ci gaba da kauracewa wuraren aikinsu da zimmar bin umurnin kungiyar ta ASUU. Ya kuma nunar da cewa babu wani hakki da malaman jami’ar Jahar Sokoto ke bin gwamnatinsa kama daga albashi ya zuwa sauran bukatu da bai yi mu su ba. Ya bayyana cewa babu wata matsala a duniya da ta gagari tattaunawar da za ta kai ga cimma maslaha, kuma ya zama wajibi a fito da matakin da zai iya zama kandagarki ga duk wani abu da ke haifar da yajin aiki a Najeriya. “Bai kamata ku biyewa uwar kungiya ta ASUU ba, saboda matsalolinsu ba su shafe ku ba. Kuna cutar da dalibanku ne kawai, kuma wannan biyayyar da kuke  ci gaba da yi na da matukar muni da nakasu ga makomar i...

Kalubalen Tsaro Da Canza Shekar Kwamishinan Tsaron Jahar Sokoto

  A daidai lokacin da matsalar tsaro ke Æ™ ara ta’azzara a jahar Sokoto, kwamishinan tsaron jahar Kanal Garba Moyi (mai ritaya) ya bayar da sanarwar aje mu Æ™ aminsa tare da ficewa daga jam’iyyar jam’iyar PDP mai mulkin jahar. A cewar tsohon kwamishinan tsaron, “akwai gaggan matsaloli da suka taka rawa wajen ficewarsa daga jam’iyayar, da suka ha É— a da sakacin gwamnan jahar, Aminu Waziri Tambuwal na watsi da dukan   shawarwarin da ake ba shi da suka shafi tsaro; kazalika da rashin sauraren Æ™ orafe- Æ™ orafen dangane da ci gaban jahar a fannoni da dama”. A ranar alhamis da ta gabata dai wasu ‘yan bindiga suka kai wani hari a garin Chakai da ke Ƙ aramar Hukumar Mulki ta Tambuwal, wadda ita ce mahaifar gwamnan jahar, in da suka sace mutum goma sha bakwai ciki har da mata da Æ™ ananan yara, tare da neman diyyar naira miliyan takwas da dubu É— ari biyar. Kazalika, sun fitar da sanarwar shirin hallaka mutanen daga gobe talata, muddin ‘yan uwan wadanda ake garkuwa da sun ba su aika...

INEC Ta Yi Watsi Da Lawan Ta Tabbatar Da Machina

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta Najeriya (INEC) ta fitar da sabuwar sanarwa a jiya alhamis 23 ga watan Yuni, 2022 da ke tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin halastaccen dan takarar kujerar dan majalisar dattijai na kasa mai wakiltar kananan hukumomin Machina da Gashuwa da Nguru da Jakusko da Yusufari da Bade da kuma Karasuwa jahar Yobe, in da kuma ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa ba ta san da wani zaben fidda gwani da aka gudanar ba koma bayan wanda ya wakana a ranar 28 ga watam Mayu. A cewar INEC babu wani dan takara da ta sani face Bashir Sheriff Machina. Tun da farko dai Sanata Ahmad Lawan ne ke wakiltar wadannan kananan hukumomin, wanda hukumar ta bayyana da cewa ya nemi mukamin shugaban kasa a maimakon matsayin da ya ke akai yanzu haka na dan majalisar dattijai. An dai jiyo shugaban jami'iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu, a wata hira da sashen Hausa na BBC na bayyana cewa ba su san da wani ba sai sanata Ahmed Lawan, abinda ya jawo cece-ku-ce....

An Kama Wasu Daliget Da Kuri'un Bogi

Har yanzu ana ci gaba da jefa kuri'a kuma kimanin jaha 14 ne suka kaɗa ƙuri'unsu a zaben fidda gwani na APC da ke gudana a Dandalin Eagles da ke Abuja. Wadannan jahohin su ne Abia da Kano da Katsina da Adamawa da Delta da Cross River da Osun da Ogun da Borno da Neja da Binuwai da sauran su. Zuwa tsakar daren jiya an dan samu tsaiko na awa guda kasancewar an samu wasu daliget da kuri'un bogi, wanda aka dakatar da zaben kafin daga baya a ka ci gaba.

Yahaya Bello Ya Caccaki Buhari

Da ya ke jawabi a lokacin da ake gudanar da shirin zaben fitar da gwani, gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello ya nemi a zabe shi domin ya magance matsalar tsaro da karancin ilmi da ake fama da su yanzu haka a Najeriya. Ya ce, "akwai takaici ace wai yanzu malaman jami'a suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune a gida kuma an kasa magance wannan matsala mai saukin magancewa". Yahaya Bello wanda ya ce ba zai jaye ma kowa a neman tikitin shugaban kasa, ya kara da cewa shi matashi ne kuma matasa ya kamata a ba dama su mulki kasar nan ba tsofaffi da suka gaji ba. Ya yabawa shugaba Buhari akan saka hannu a kan dokar ba matasa damar tsayawa takara, in da ya ce abu ne mai kyau. Ya yi kira ga mata da sauran 'yan Najeriya da ya ce ana zalunta da su zabe shi. Dan takarar ya ce "yanzu haka babu tsaro ko kadan kuma an kyale, ana kashe mutane ana kona mu su dukiya kuma ana kallo an zura ido".

'Yan Takarar Shugaban Kasa Sun Fara Janye Ma Bola Tinubu

Kawo yanzu dai akwai masu neman mukamin shugaban kasa da suka fito kafin fara jefa kuri'a suka bayyana cewa sun janye takararsu kuma sun marawa tsohon gwamnan jahar Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Daga cikin su akwai gwamnan jahar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar da Fayemi Kayode da Ajayi Boroffice da tsohon kakakin majilasar wakilai Dimeji Bokole da kuma Gidein Akpabio. Amma Pasto Tunde Bakari ya bayyana cewa shi kam ba zai jaye ma kowa da ga cikin 'yan takara ba, kasancewar "ba su da kyakkyawar manufar gina kasa face rusa ta", in ji shi. Akwai 'yan takara da dama da ya zu haka su ke jiran a fara kada kuri'a da suka hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da sanata Ahmed Yariman Bakura da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rotimi Amechi da sauran su. Zamu kawo mu ku karin labari nan gaba.

"Ba Ni Goyon Bayan Kowane Dan Takara" - Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bauyana cewa bai zabo kowane dan takara ba, akan haka a bar daliget su zabi wanda 'yan jam'iyya ke so. Bayan ganawa da shugaban kasan jim kadan bayan da shugaban jam'iyyar APC Sanata Abdullahi Adamu ya ayyana Sanata Ahmed Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa na APC, karkashin jagorancin gwamnan jahar Kebbi Atiku Bagudo, sun ce sun tabbatar ma shugaba Buhari cewa har yanzu suna kan bakansu na mika mulki ga kudu. Wannan dai ya nuna daga gobe takara jam'iyyar APC za ta gudanar da zaben fitar da gwani.

Gwamnonin APC Da Sauran Masu Takara Ba Su Amince Da Zabin Ahmad Lawan Ba

Gwamnonin jam'iyar APC da masu takarar neman mukamin shugaban kasa sun ja daga akan wannan mataki na tsayar da Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa. Sun nemi dole mulki ya koma kudu kuma a gudanar da zaben fidda gwani. Labarin da ke shigowa yanzu haka ya nunar da cewa za a fafata a zaben fidda gwani tsakanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Tinubu da Kayode Fayemi da David Umahi da sauran su a Dandalin Eagles da ke Abuja a gobe talata. Za ku ji sauran bayani daga baya.