Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Kudu maso Gabas hatta a cikin makon da za a gudanar da babban zaɓen 2023. Rahotanni daga yankin sun ce wasu da ba gano ba sun kashe Mista Oyibo Chukwu, ɗan takarar ɗan majalisar dattawa mazabar Enugu ta gabas a ranar Asabar, sa’o’i 48 kafin gudanar da zaɓen. An kashe Chukwu ne tare da wasu magoya bayansa biyar a ƙaramar hukumar Awkunanaw ta Enugu a lokacin da yake dawowa daga wani gangamin yaƙin neman zaɓe. An kuma ce masu kisan sun kona shi da magoya bayansa bayan sun tare da shi a cikin motarsa. Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Labour, Chijioke Edeoga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jam’iyyun siyasa na yi wa ‘ya’yan jam’iyyarsa kisan gilla, waɗanda ke ganin barazana ce ga bunƙasar jam’iyyar a jihar. Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, ya fito ne daga yankin Kudu maso Gabas, wanda tashin hankali ya zama ruwan dare, tun kafin lokacin zaɓe. Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sha alwa...