Gwamnatin jahar Kaduna ta fitar da sanarwar cewa annobar korona ta sake dawowa a jahar. Gwamnatin jahar ta tabbara da samun sabbin kamuwa da cutar har mutum 64, wanda a cewar ta tuni su ma a ka kebe su. An kuma jiyo gwamnan jahar Malam Nasiru El-Rufa'i, na cewa muddin jama'ar jahar suka ci gaba da yin biris da dokokin da aka shata musu to babu makawa gwamnatin za ta sake kulle su ruf har sai lokacin da annobar Covid-19 din ta lafa. Gwamnan ya ce yana mamakin yadda al'umma ke watsi da ka'idojin da tuni aka san da su, na rage cin koso da sanya takunkumi da kuma yawaita wanke hannuwa. Jahar Kaduna na cikin jahohin da suka fuskanci dokar kulle sakamkon barkewar annobar ta korona a watannin baya. To sai dai wannan gargadi na gwamnatin jahar ya gamu da suka, musamman ga wadanda ke kallon kalaman a matsayin na 'yan boko.