Skip to main content

Maina Ya Kife A Kotu

 Tsohon shugaban kwamitin hana badakala a hukumar fansho ta kasa Abdulrasheed Maina, ya fadi a kotun birnin tarayya a Abuja, daidai lokacin da ake tsaka da yi masa shari'a.

Tsohon shugaban kwamitin dai ana tuhumar sa ne da badakalar da ta danganci batar da kimanin naira biliyan biyu sa'adda da ya ke jagorancin kwamitin. Tun daga lokacin da aka kai shi kotu Maina ya yi batan dabo bayan da ya samu beli.

Bayan kwashe tsawon lokaci ana neman sa daga bisa ni an yi nasarar gano shi a kasar Jamhuriyar Nijar.

Wannan al'adar faduwa a gaban kwamitocin bincike ba bakuwa ba ce a Najeriya, in da ko watannin baya shugaban kwamitin Hukumar Raya Yankin Naija Delta (NDDC) farfesa Podei ya yi zaman tsumma a kwando, lokacin da yake amsa bahasi a gaban kwamitin majalisar wakilai na kasa dangane da badakalar da ake zargin sa da hannu na karkata kwangiloli da kudaden hukumar zuwa wata hanya daban.

Comments