Skip to main content

Mutum 64 Sun Kamu Da Korona A Kaduna - El-Rufa'i

Gwamnatin jahar Kaduna ta fitar da sanarwar cewa annobar korona ta sake dawowa a jahar.
Gwamnatin jahar ta tabbara da samun sabbin kamuwa da cutar har mutum 64, wanda a cewar ta tuni su ma a ka kebe su.
An kuma jiyo gwamnan jahar Malam Nasiru El-Rufa'i, na cewa muddin jama'ar jahar suka ci gaba da yin biris da dokokin da aka shata musu to babu makawa gwamnatin za ta sake kulle su ruf har sai lokacin da annobar Covid-19 din ta lafa.
Gwamnan ya ce yana mamakin yadda al'umma ke watsi da ka'idojin da tuni aka san da su, na rage cin koso da sanya takunkumi da kuma yawaita wanke hannuwa.
Jahar Kaduna na cikin jahohin da suka fuskanci dokar kulle sakamkon barkewar annobar ta korona a watannin baya.
To sai dai wannan gargadi na gwamnatin jahar ya gamu da suka, musamman ga wadanda ke kallon kalaman a matsayin na 'yan boko.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

Binani Na Neman Kotu Ta Tabbatar Da Ita Wadda Ta Lashe Zaɓen Adamawa

Magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Adamawa a ranar Litinin sun fito kan tituna domin nuna adawa da ayyana Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan Adamawa. Sai dai ita Binani ta buƙaci wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) daga sauya matakin da aka ɗauka na ayyana ta da a ka yi a matsayin wadda ta lashe zaɓen.  A wata buƙata da ta shigar a ranar Litinin, mai neman izinin kotun ya nemi izinin kotun ta ba ta damar shigar da buƙatar neman umarnin haramtawa INEC daga ɗaukar duk wani mataki na watsi da sanarwar da aka yi a ranar 16 ga Afrilu da Kwamishinan zaɓen jahar, Barista Hudu Ari ya ayyana ta a matsayin wadda ta samu ƙuri'u mafifi rinjaye kuma ta lashe zaɓen alhali ba a kammala tattara sakamakon zaɓen gaba ɗaya ba. Ta kuma nemi a ba da umarnin hana hukumar zabe ta INEC, da wakilinta nadawa ko kuma duk wanda ke wakiltarta daukar wasu matakai na bayyana wanda ya lashe zaben gwamna da ak...