Skip to main content

Kotu Ta Aminta Da Rataye Maryam Sanda

Yau din nan kotun birnin tarayya Abuja ta tabbatar da hukunci da kotun baya ta yanke na rataye Maryam Sanda.
Kotun ta bayyana cewa hukuncin da aka yanke ma ta tun da farko babu kuskure cikin sa saboda haka ta bayar da umurnin gaggauta rataye ta.
An dai samu Maryam sanda da laifin kashe mijinta har lahira ta hanyar daba masa wuka. Amma ta daukaka kara kan hukuncin da aka yanke ma ta a watan Janairun wannan shekara ta 2020.

Comments