Skip to main content

Posts

CBN Insists On Deadline Despite Court Order

The Central Bank of Nigeria CBN has insisted that its February 10th deadline for the validity of old naira notes still stands. The CBN governor, Godwin Emefiele, made the disclosure while briefing the diplomatic community at the ministry of foreign affairs in Abuja. The development comes despite the ex-parte order of the Supreme Court which restrained the federal government from implementing the February 10th deadline, pending the hearing of the matter on February 15th. Emefiele said the situation is substantially calming down since the commencement of over-the-counter payments to complement ATM disbursements and the use of super-agents. He added that there is no need to consider any shift from the deadline of February 10th.

Filin Jiragen Sama Na Malam Aminu Kano Zai Ci Naira Biliyan 700

Ministan suhurin jiragen sama Alhaji Hadi Sirika, ya bayyana cewa majalisar zartaswata Æ™asa ta amince da ware fiye da naira biliyan É—ari bakwai domin aikin kwangilar gyaran filin sauka da tashin jiragen na sama na duniya na Malam Aminu Kano, wanda ya ce za kammala a cikin shekara É—aya rak. Majalisar zartaswa ta Æ™asa ta kuma amince da ware naira biliyan É—ari da goma sha bakwai domin gudanar da kwangilar gina cibiyar bincike akan man fetur ta Oloibir a yankin Naija Delta. Ministan Æ™asa a ma’aikatar albarkatun man fetur, Timipre Sylva ne ya shaidawa ‘yan jaridar fadar shugaban Æ™asa hakan, inda ya ce za a kammala aikin kwangilar a cikin shekaru biyu da rabi. Ya ce tun a 1980 gwamnatin Alhaji Shehu Aliyu Shagari ta soma aikin, amma daga bisani aka yi watsi da shi wanda a yanzu zai zama É—aya daga cikin manyan ayyukan da za a ci ga da tunawa da shugaba Muhammadu Buhari a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur.

Kotu Ta Tabbatar Da Peter Obi Matsayin ÆŠan Takarar Jam'iyyar LP

Kotun É—aukaka Æ™ara mai mazuninta a Abuja ta yi watsi da Æ™arar da jam’iyyar APM ta shigar inda take neman a hanawa Peter Obi na jam’iyyar Labour damar tsayawa takara a zaÉ“e mai zuwa. WaÉ—anda ake Æ™arar su ne Hukumar ZaÉ“e mai zaman kanta, INEC da jam’iyyar Labour da kuma É—an takararta Mista Peter Obi. Da ta ke yanke hukuncin tare da taimakon alÆ™alai uku, mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta amince da yin watsi da shari’ar a dalilin rashin cikakkun hujjoji. AlaÆ™alan kotun sun nemi masu saka Æ™arar da su biya waÉ—anda ake Æ™ara tarar naira dubu É—ari biyu a dalilin É“ata mu su lokaci.

Tinubu Zai Dawo Da Tsoffin KuÉ—i - El-Rufai

Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ya roƙi jama'a cewa kowa ya yi amfani da tsoffin kuɗi daga nan har shekara huɗu. A cikin wani gajeren bidiyo mai tsawon minti huɗu da daƙiƙa talatin da bakwai, an ga gwamnan na bayyana cewa ya bayar da umurnin duk wani ɗan jahar da ke kasuwanci kada ya fasa amfani da tsoffin kuɗaɗe. "Duk wani ɗan jahar Kaduna daga nan har shekara huɗu in dai an zaɓi APC, Uba zai mayar masa da kuɗinsa". In ji gwamna El-Rufai. A cewarsa wannan saƙo ne daga ɗan takarar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, wanda kuma in ji gwamnan da an zaɓi Tinubu zai sauya wannan tsarin canjin fasalin kuɗi nan take in da zai dawo da tsoffin da mutane ba su kai banki ba. Saboda haka ya umurci jama'a da kada kowa ya kai kuɗinsa banki. Ya ƙara da cewa da zarar an zaɓe su, ya ɗauki alkawarin amsar kuɗin mutane ya tilasta Babban Bankin Najeriya CBN ya canza su musu da sababbi. Ya ci gaba da cewa, "Ku gaya ma kowane ɗan kasuwa, ya karɓi tsohon...

PDP Na Shirin Korar Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya shigar da Æ™ara domin hana wani sabon yunÆ™urin jam’iyyar PDP dakatar da shi daga cikinta, kuma ya buÆ™aci kotun da ta É—auki mataki ga duk masu wannan aniya.  ÆŠaya daga cikin jigajigan jam'iyyar PDP da suka mayar da martani kan Æ™arar da gwamna Wike ya shigar, Mahdi Shehu, ya mayar da martani a ranar Litinin da ta gabata inda ya wallafa a shafinsa na twitter wata sanarwa cewa, “Wike ya shigar da Æ™ara kan jam’iyyar PDP mai lamba FHC/ABJ/CS/139/2023 ta hannun lauyoyinsa, DY Musa (SAN);  Douglas Moru, da C. C. Chibuike, yana neman a ba shi umarnin hana a kore shi daga PDP.”   Wike dai ya yi ta famar ruguza jam’iyyar har ma ya rasa inda za shi. Gwamnan na Ribas ya zamewa jam'iyyar PDP Æ™adangaren bakin tulu, irin yadda ya ke uwa da makarbiya tun bayan da dangantaka ta soma tsami tsakaninsa da wasu jigajigan jam'iyyar ciki kuwa har da gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.  

Japan Ƙasar Da Kowa Tsoho

A Æ™asar Japan da ke gabashin Asiya, adadin haihuwa a shekara ya ragu zuwa kasa da dubu 800 a karon farko a shekarar 2022. Ya zuwa farkon shekarar 2023, kashi 29 na al'ummar Japan mai mutane miliyan 124.77 na da shekaru 65 ne ko sama da haka, kuma kashi 11.6 na tsakanin shekarun 0 da 14. Japan ita ce Æ™asa ta farko a duniya bisa ga jimillar yawan jama'a masu shekaru 65 zuwa sama. Firaministan Æ™asar, Kishida Fumio ya sanar da cewa Japan na gab da rasa ayyukanta na zamantakewar al’umma sakamakon raguwar yawan haihuwa kuma a bana za su mai da hankali kan manufofin renon yara. Hukumar Kula da Yara da Iyali, mai alaÆ™a da gwamnatin Æ™asar za ta fara aiki a watan Afrilu. Kisida ya bayyana cewa suna shirin ruÉ“anya kasafin kuÉ—in manufofin da suka wajaba daga yanzu zuwa watan Yuni. Duk da ci gaban da Æ™asar Japan ke da shi a fannonin Æ™ere-Æ™ere da fasaha, rashin wadattatun matasa ya sa tana fuskantar matuÆ™ar barazana ga Æ™arewar jama'a.

Jam'iyyu 13 Sun Yi Barazanar Ƙauracewa Zaɓe A Najeriya

Gamayyar jam'iyyun adawa 13 sun bayyana cewa za su ƙauracewa shiga zaɓe muddin Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙara wa'adin amfani da tsofaffin kuɗaɗe daga lokacin da aka ɗiba tun da farko. Shugaban jam'iyyar AA Kennetth Udeze ne ya fitar da wannan sanarwa, in da ya ce canjin fasalin kuɗi da CBN ya fito da shi zai haifar da babban tasiri a tattalin arziki da fannin tsaro kana sun kai matsayar watsi da sabon matakin da gwamnonin APC suka ɗauka da suka haɗa da na Kaduna, Malam Nasiru El-rufai da na Zamfara Bello Mutawalle da na Kogi Yahaya Bello, na maka shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gaban kotu kan sauya takardun kuɗi da ya yi. A Najeriya akwai jerin jam'iyyu 18 da za su fafata a babban zaɓe mai zuwa sai dai 13 daga ciki sun yi barazanar janye jikinsu daga shiga zaɓen muddin aka ƙara lokacin amfani da tsofaffin kuɗaɗe. Menene ra'ayinka kan wannan batu?

Yadda Masu KuÉ—i Da Ruwa Suka Cika Harabar ATM

Rahotonni da ke ci gaba da shigo muna yanzu haka, na nuni da cewa É—aruruwan mutane na ta yi dogayen  layuka a gaban na'urar cirar kuÉ—i ta ATM da ke bankuna, inda suke amfani da wani salo na biyan mutane domin su ciro mu su kuÉ—i. Wani da muka zanta da shi mai suna Lawal Mai Masara, ya shaida muna cewa, tun jiya ya ke kan layi, kuma har yanzu bai kai ga samun kuÉ—in ba saboda masu sana'ar POS da masu kwashe kuÉ—i su sake adanawa sun cika ko'ina. "Za ka ga mutane riÆ™e da katunan cirar kuÉ—i fiye da 10 inda suke tura ma wasu kuÉ—i su rarraba musu katunan domin a cire mu su kuÉ—in a ATM daga baya su bayar da naira dubu akan duk dubu goma da aka cire mu su". In ji shi. Mutumin ya Æ™ara da cewa wannan na daga cikin manyan dalilan da suka haddasa Æ™arancin kuÉ—i tsakanin mutane a Najeriya.musamman arewa. Wannan sabon matakin ya nuna irin yadda mutane ke jefa kansu a halin tasku ta hanyar ci gaba da kwashe kuÉ—aÉ—en da jama'a ya kamata su samu. Wani ganau...

Wike Ya Tona Magoya Bayan Atiku A Fadar Shugaban Ƙasa

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun tabbatar masa da cewa É—an takarar shugaban Æ™asa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar da magoya bayansa, na taÆ™ama da cewa ba sa buÆ™atar goyon bayan gwamnonin G5 kafin su ci nasara zaÉ“e, saboda wasu tsiraru a fadar shugaban Æ™asa sun ba su tabbacin samun nasara a zaÉ“en shugaban Æ™asa mai zuwa. Jaridar POLITICS NIGERIA  ta ruwaito cewa gwamnan yayi magana ne a garin Ibaka a yayin gangamin yaÆ™in neman zaÉ“en jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas na Æ™aramar hukumar Okrika a ranar Juma’a. "Na ce an ba su tabbaci, amma wannan zaÉ“en ba zai dogara ne akan wannan tabbacin ba, yana kan tabbacin mutane ne,” in ji Wike. Gwamna Wike dai ya dage cewa har yanzu Atiku na buÆ™atar jihar Ribas don samun nasara ko kuma ya faÉ—i zaÉ“e a 2023. A cewarsa, “ko kuna so ko ba ku so, dole ne ku buÆ™aci jihar Ribas. Idan ba ku buÆ™atar Jihar Ribas to dole ne ku sha Æ™asa. Idan kun ce ba ku son mu, lallai kuwa za ku gaz...

Canjin KuÉ—i Alfanu Ne - Peter Obi

ÆŠan takarar shugaban Æ™asa a jam'iyyar Labour Party Mista Peter Obi, ya shawarcin 'yan Najeriya da su rungumi sabon tsarin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito da shi na canjin fasalin kuÉ—i, in da ya ce yana da muhimmanci. Ya roÆ™i 'yan Najeriya da su marawa tsarin baya, wanda a cewar sa  ba Najeriya ce ta farko a canza fasalin kuÉ—i ba a duniya, sai dai wannan ya zo da wahala ga jama'a amma kuma yana da matuÆ™ar amfani ga tattalin arzikin Æ™asa  da walwalar jama'a duk da akwai buÆ™atar a inganta shi. Mista Obi ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a Æ™arshen makon nan. Peter Obi dai ya taÉ“a zama mataimakin É—an takarar shugaban Æ™asa, Alhaji Atiku Abubakar a 2019 kafin yanzu shi ma ya fito neman wannan kujera a babban zaÉ“e mai zuwa.