Hukumar Bayar da Tallafin Ƙaro Karatu ta Jihar Sokoto na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa ɗalibai da bunƙasa harkokin ilimi a faɗin jihar, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Murtala Abdulkadir Dan Iya. Murtala Dan Iya da gwamnan jihar Sokoto Dakta Ahmed Aliyu Tun bayan hawansa wannan muƙami, hukumar ta mayar da hankali wajen sauƙaƙa wa ɗalibai samun tallafin karatu domin ci gaba da karatunsu a manyan makarantu daban-daban ci da wajen Najeriya. Masu amfani da shirin sun bayyana cewa tallafin na taimakawa wajen rage wa iyaye da ɗalibai nauyin kuɗaɗen karatu da sauran buƙatun makaranta. Gwamnatin Jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dakta Ahmed Aliyu ta ci gaba da nuna muhimmanci ga fannin ilimi ta hanyar tallafawa shirye-shiryen da suka shafi ci gaban ɗalibai da inganta harkokin makarantu da samar da kayan aiki da kujeru da tura malaman jami'o'i n jihar waje domin karo karatu, matakin da shugaban hukumar karo ilimin ya dage wajen ganin ya samu nasar...