Skip to main content

Posts

Showing posts from June 15, 2026

Ayyukan Mataimakin Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Idris Muhammad Gobir Danchadi

Gwamnatin Jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dr. Ahmed Aliyu Sokoto da mataimakinsa Alhaji Idris Muhammad Gobir, wanda ya fito daga yankin gabashin jihar, na aiwatar da manyan ayyukan ci gaba ta hanyar amfani da tsarin nan na Gwamnatin Sokoto na 9-Point Smart Agenda . Wasu daga cikin ayyukan da Alhaji Idris Gobir mataimakin gwamnan jihar Sokoto ya sanyawq gaba tare da hadin gwiwar gwamna sun hada da: Karfafa Tsaro da Tallafin Jami'an Sa-Kai Yankin gabashin Sokoto da da ya haɗa da Isa da Sabon Birni da Goronyo da kuna Gwadabawa ya dade yana fama da matsalar tsaro. Alhaji Idris Gobir yana jagorantar harkokin tsaro ta hanyar 1. Saye da rarraba motocin aiki da babura ga jami'an tsaro da jami'an sa-kai na yankin. 2. Samar da kudaden alawus na mako-mako domin karfafa gwiwar masu gadin daji da kauyuka. Gyaran Hanyoyi da Kayan More Rayuwa Mataimakin gwamnan, shi ne kuma ke kula da Ma'aikatar Ayyuka ta jihar, yana tabbatar da cewa an karkata ayyukan...