Skip to main content

Ayyukan Mataimakin Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Idris Muhammad Gobir Danchadi

Gwamnatin Jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dr. Ahmed Aliyu Sokoto da mataimakinsa Alhaji Idris Muhammad Gobir, wanda ya fito daga yankin gabashin jihar, na aiwatar da manyan ayyukan ci gaba ta hanyar amfani da tsarin nan na Gwamnatin Sokoto na 9-Point Smart Agenda.

Wasu daga cikin ayyukan da Alhaji Idris Gobir mataimakin gwamnan jihar Sokoto ya sanyawq gaba tare da hadin gwiwar gwamna sun hada da:

Karfafa Tsaro da Tallafin Jami'an Sa-Kai

Yankin gabashin Sokoto da da ya haɗa da Isa da Sabon Birni da Goronyo da kuna Gwadabawa ya dade yana fama da matsalar tsaro. Alhaji Idris Gobir yana jagorantar harkokin tsaro ta hanyar

1. Saye da rarraba motocin aiki da babura ga jami'an tsaro da jami'an sa-kai na yankin.

2. Samar da kudaden alawus na mako-mako domin karfafa gwiwar masu gadin daji da kauyuka.

Gyaran Hanyoyi da Kayan More Rayuwa

Mataimakin gwamnan, shi ne kuma ke kula da Ma'aikatar Ayyuka ta jihar, yana tabbatar da cewa an karkata ayyukan kwalta zuwa yankunan karkara:

1. Ana gudanar da gyare-gyaren hanyoyin da suka hada manyan garuruwan gabashin Sokoto domin saukaka zirga-zirgar amfanin gona da kasuwanci.

2. Tursasawa 'yan kwangila su gudanar da ayyuka masu inganci ba tare da nuna son kai ba.

Lafiya da Yaki da Cututtuka

A matsayinsa na mai kula da tsare-tsaren gwamnati, yana hada gwiwa da manyan kungiyoyin kasa da kasa kamar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da UNICEF) domin:

1. Tura jami'an kiyyon lafiya na musamman don kai magunguna da allurar riga-kafi kyauta ga yara da mata a yankunan da ke da wuyar isa a gabashin Sokoto.

Tare da gyara da kuma samar da kayan aiki ga rukunonin asibitocin karkara (Primary Health Centres).

Agajin Gaggawa ga 'Yan Gudun Hijira

Saboda hare-haren 'yan fashin daji da suka raba mutane da dama da muhallansu a yankin:

1. Alhaji Idris Gobir yana jagorantar rarraba kayan abinci, katifu, da magunguna ga sansanonin 'yan gudun hijira dake cikin kananan hukumomin yankin.

2. Yana tattaunawa da kungiyoyin agaji na kasa da kasa don gina musu matsugunai na din-din-din.

Mataimakin gwamnan yana amfani da sabon rahoton kididdigar yaƙi da fatara wanda Hukumar Kididdiga ta Jiha ta fitar, domin gano ainihin bukatun kowane kauye dake gabashin Sokoto domin.
Lokacin da muka ziyarce shi mun ga shaida da idonmu ya kan kwashe dare yana sauraren korafin talakawan da yake wakilta, ciki kuwa har da kai ziyarar ga talaka da yi musu jaje da bayar da tallafin kudi da abinci ga mabukata halin da aka san shi da shi yun kafin ya zama mataimakin gwamnan jihar Sokoto.

Comments

Popular posts from this blog

Iran seeks talks with us after threat of attack – Trump

U.S. President Donald Trump has said that Iranian authorities have contacted the United States to seek talks, following his threat to take military action over the killing of protesters in the country. Trump made the statement while speaking to journalists, saying that a meeting between the two sides has already been planned, but that the United States might take some action before the meeting takes place. Meanwhile, a human rights organization in Iran says it has confirmed the deaths of nearly 500 people since the outbreak of the protests. Likewise, some circulating video clips show a site outside Iran where bodies are being kept, with people going there to search for the remains of their relatives who have gone missing.

WHEN LIES GO VIRAL: DEFENDING TRUTH IN NIGERIA AND WEST AFRICA’S DIGITAL PUBLIC SPHERES

Across Nigeria and West Africa, digital technology has reshaped how citizens engage with information, governance, and public debate. Mobile phones and social media platforms have become dominant sources of news, especially for young people and communities with limited access to traditional media. While this transformation has expanded civic participation and freedom of expression, it has also intensified the spread of misinformation, posing serious risks to democracy, public health, and social cohesion. Misinformation is no longer a marginal problem. It is a structural challenge that affects elections, security, development communication, and trust in public institutions. Addressing it requires coordinated action that combines ethical journalism, media literacy, platform accountability, and evidence based policy responses. THE DIGITAL INFORMATION LANDSCAPE IN NIGERIA AND WEST AFRICA Nigeria is Africa’s most populous country and one of its most digitally active societies. So...

Murtala Abdulkadir Dan Iya Gambun Sakkwatawa

Alhaji Murtala Abdulkadir Dan Iya ya shahara wajen ayyukan jinƙai a Jihar Sokoto tsawon  shekarun ya zuwa yanzu. Alhaji Murtala Abdulkadir Dan Iya shugaban Hukumar Bayar Da Tallafin Ƙaro Karatu ta Jihar Sokoto  A tattaunawar da jaridar Tantabara News ta yi da Nura Muhammad Chiso, wanda ke jagorancin daya daga cikin ƙungiyoyin Alhaji Murtala Abdulkadir Dan Iya, mai suna da ke bayar da tallafi da wayar da kan al'umma a jihar ta Sokoto, ya bayyana tarin manyan tallafan da wannan shahararren ɗan kasuwa, kuma ɗan siyasa ya yi wa dubban mutane mabukata a jihar, lamarin da ya ƙara ɗaukaka darajar sunansa a cikin jihar da ma wajenta. N ura Muhammad Chiso  Nura Muhammad Chiso ya ce, "wannan aikin alheri na shugaban Hukumar Bayar Da Tallafin Ƙaro Karatu ta Jihar Sokoto, wani babban aikin alheri ne da ya gane dubban jama'a talakawa har hakan ya sa suke kiran sa da gambun Sakkwatawa saboda faranta musu rai da yake yi". Ga wa...