Skip to main content

Posts

Showing posts from June, 2026

Sakon Alhaji Murtala Abdulkadir Dan Iya na goyon baya da taya murna ga gwamnan jihar Sokoto

Cikin ikon Allah mun cika shekara uku da zaɓen mai girma gwamnan jihar Sokoto Alhaji Dakta Ahmed Aliyu (PhD, ACIT, FCNA) da ya lashe da gagarumin rinjaye. Babu shakka mun yaba da irin namijin ƙoƙarin mai girma gwamna ta ɓangarorin kiyyon lafiya da ilimi da noma da samar da aikin yi, da gina hanyoyi da asibitoci da samar da magunguna da kayan aiki a birni da kewaye. Tamkar yadda muka yi tsayin daka har muka cimma wannan nasara da farko, a yanzu haka muna bayar da cikakken goyon bayanmu domin sake samun nasararka a karo na biyu in sha Allahu. Muna godiya ga jama'ar jihar Sokoto da irin goyon bayan da suke ba mu kuma muna tare da su tamkar tsintsiya madaurinki ɗaya. Na gode. Sako daga Alhaji Murtala Abdulkadir Dan Iyan Jarman Daular Usmaniyya Shugaban Hukumar Bayar da Tallafin Ƙaro Karatu ta Jihar Sokoto.