Skip to main content

Murtala Abdulkadir Dan Iya Ya Ci Gaba da Ƙarfafa Harkokin Ilimi da Haɗin Kan Al'umma a Sokoto


Hukumar Bayar da Tallafin Ƙaro Karatu ta Jihar Sokoto na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa ɗalibai da bunƙasa harkokin ilimi a faɗin jihar, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Murtala Abdulkadir Dan Iya.
Murtala Dan Iya da gwamnan jihar Sokoto Dakta Ahmed Aliyu 
Tun bayan hawansa wannan muƙami, hukumar ta mayar da hankali wajen sauƙaƙa wa ɗalibai samun tallafin karatu domin ci gaba da karatunsu a manyan makarantu daban-daban ci da wajen Najeriya. Masu amfani da shirin sun bayyana cewa tallafin na taimakawa wajen rage wa iyaye da ɗalibai nauyin kuɗaɗen karatu da sauran buƙatun makaranta.
Gwamnatin Jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dakta Ahmed Aliyu ta ci gaba da nuna muhimmanci ga fannin ilimi ta hanyar tallafawa shirye-shiryen da suka shafi ci gaban ɗalibai da inganta harkokin makarantu da samar da kayan aiki da kujeru da tura malaman jami'o'i n jihar waje domin karo karatu, matakin da shugaban hukumar karo ilimin ya dage wajen ganin ya samu nasara.
A cewar masu ruwa da tsaki, wannan ya nuna yadda gwamnati ke kallon ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban al'umma.
Baya ga ayyukan da suka shafi tallafin karatu, Murtala Abdulkadir Dan Iya ya kasance yana gudanar da ziyarce-ziyarcen tuntuba ga sarakunan gargajiya, malamai da shugabannin al'umma a sassa daban-daban na jihar. Ana ganin waɗannan ziyarce-ziyarcen a matsayin wata hanya ta ƙarfafa haɗin kai da karɓar shawarwari daga jama'a domin inganta ayyukan gwamnati.
Wannan ya karawa MD Alhaji Murtala Abdulkadir Dan Iya kina a idon manyan Najeriya ciki har da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da ya yaba irn kwazonsa wajen xi gaba da raya ilmi a jihar Sokoto.
MD Murtala Abdulkadir Dan Iya Da mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima 
Wasu daga cikin shugabannin gargajiya da malaman addini da suka yi mu'amala da hukumar sun yaba da irin yadda ake neman ra'ayoyinsu kan batutuwan da suka shafi ilimi da ci gaban al'umma. Sun ce hakan na taimakawa wajen samar da fahimtar juna tsakanin gwamnati da jama'a.
Haka kuma, hukumar ta shiga cikin shirye-shiryen wayar da kan matasa kan muhimmancin ilimi da neman ilimin zamani tare da na addini, domin samar da matasa masu ilimi da kishin ci gaban jiharsu.
Masana harkokin ilimi sun bayyana cewa ci gaba da tallafawa ɗalibai da samar da damarmakin karatu na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen samar da ƙwararrun ma'aikata da shugabanni a nan gaba.
Al'ummar jihar Sokoto da dama na fatan ganin an ci gaba da ƙarfafa irin waɗannan shirye-shirye da nufin faɗaɗa damar ilimi ga matasa, musamman waɗanda ke fitowa daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi, domin su samu damar cimma burinsu na ilimi da rayuwa.

Comments

Popular posts from this blog

Iran seeks talks with us after threat of attack – Trump

U.S. President Donald Trump has said that Iranian authorities have contacted the United States to seek talks, following his threat to take military action over the killing of protesters in the country. Trump made the statement while speaking to journalists, saying that a meeting between the two sides has already been planned, but that the United States might take some action before the meeting takes place. Meanwhile, a human rights organization in Iran says it has confirmed the deaths of nearly 500 people since the outbreak of the protests. Likewise, some circulating video clips show a site outside Iran where bodies are being kept, with people going there to search for the remains of their relatives who have gone missing.

WHEN LIES GO VIRAL: DEFENDING TRUTH IN NIGERIA AND WEST AFRICA’S DIGITAL PUBLIC SPHERES

Across Nigeria and West Africa, digital technology has reshaped how citizens engage with information, governance, and public debate. Mobile phones and social media platforms have become dominant sources of news, especially for young people and communities with limited access to traditional media. While this transformation has expanded civic participation and freedom of expression, it has also intensified the spread of misinformation, posing serious risks to democracy, public health, and social cohesion. Misinformation is no longer a marginal problem. It is a structural challenge that affects elections, security, development communication, and trust in public institutions. Addressing it requires coordinated action that combines ethical journalism, media literacy, platform accountability, and evidence based policy responses. THE DIGITAL INFORMATION LANDSCAPE IN NIGERIA AND WEST AFRICA Nigeria is Africa’s most populous country and one of its most digitally active societies. So...

Murtala Abdulkadir Dan Iya Gambun Sakkwatawa

Alhaji Murtala Abdulkadir Dan Iya ya shahara wajen ayyukan jinƙai a Jihar Sokoto tsawon  shekarun ya zuwa yanzu. Alhaji Murtala Abdulkadir Dan Iya shugaban Hukumar Bayar Da Tallafin Ƙaro Karatu ta Jihar Sokoto  A tattaunawar da jaridar Tantabara News ta yi da Nura Muhammad Chiso, wanda ke jagorancin daya daga cikin ƙungiyoyin Alhaji Murtala Abdulkadir Dan Iya, mai suna da ke bayar da tallafi da wayar da kan al'umma a jihar ta Sokoto, ya bayyana tarin manyan tallafan da wannan shahararren ɗan kasuwa, kuma ɗan siyasa ya yi wa dubban mutane mabukata a jihar, lamarin da ya ƙara ɗaukaka darajar sunansa a cikin jihar da ma wajenta. N ura Muhammad Chiso  Nura Muhammad Chiso ya ce, "wannan aikin alheri na shugaban Hukumar Bayar Da Tallafin Ƙaro Karatu ta Jihar Sokoto, wani babban aikin alheri ne da ya gane dubban jama'a talakawa har hakan ya sa suke kiran sa da gambun Sakkwatawa saboda faranta musu rai da yake yi". Ga wa...