Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour Party Mista Peter Obi, ya shawarcin 'yan Najeriya da su rungumi sabon tsarin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito da shi na canjin fasalin kuɗi, in da ya ce yana da muhimmanci. Ya roƙi 'yan Najeriya da su marawa tsarin baya, wanda a cewar sa ba Najeriya ce ta farko a canza fasalin kuɗi ba a duniya, sai dai wannan ya zo da wahala ga jama'a amma kuma yana da matuƙar amfani ga tattalin arzikin ƙasa da walwalar jama'a duk da akwai buƙatar a inganta shi. Mista Obi ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a ƙarshen makon nan. Peter Obi dai ya taɓa zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar a 2019 kafin yanzu shi ma ya fito neman wannan kujera a babban zaɓe mai zuwa.