Skip to main content

Posts

"Ba Ni Goyon Bayan Kowane Dan Takara" - Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bauyana cewa bai zabo kowane dan takara ba, akan haka a bar daliget su zabi wanda 'yan jam'iyya ke so. Bayan ganawa da shugaban kasan jim kadan bayan da shugaban jam'iyyar APC Sanata Abdullahi Adamu ya ayyana Sanata Ahmed Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa na APC, karkashin jagorancin gwamnan jahar Kebbi Atiku Bagudo, sun ce sun tabbatar ma shugaba Buhari cewa har yanzu suna kan bakansu na mika mulki ga kudu. Wannan dai ya nuna daga gobe takara jam'iyyar APC za ta gudanar da zaben fitar da gwani.

Gwamnonin APC Da Sauran Masu Takara Ba Su Amince Da Zabin Ahmad Lawan Ba

Gwamnonin jam'iyar APC da masu takarar neman mukamin shugaban kasa sun ja daga akan wannan mataki na tsayar da Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa. Sun nemi dole mulki ya koma kudu kuma a gudanar da zaben fidda gwani. Labarin da ke shigowa yanzu haka ya nunar da cewa za a fafata a zaben fidda gwani tsakanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Tinubu da Kayode Fayemi da David Umahi da sauran su a Dandalin Eagles da ke Abuja a gobe talata. Za ku ji sauran bayani daga baya.

Stepping Down Not The Right Option - Osinbajo

Vice president Yemi Osinbajo has denied reports that he intends to step down for a certain presidential aspirant ahead of the presidential primary of the All Progressives Congress (APC). The denial is contained in a statement by the chairman of Osinbajo’s campaign council, Richard Akinnola on Sunday. According to the statement, the people behind the speculation are “afraid of the huge political support base of the Vice President, Prof. Yemi Osinbajo,” adding that the VP is ready for the presidential primary scheduled to hold between June 6 and 8. The campaign council “welcomes our distinguished delegates from across the country to Abuja for our presidential primaries. “As you settle down in Abuja, we implore you to kindly disregard various fake news making the rounds that Prof. Yemi Osinbajo has stepped down. “Osinbajo would be hoping to clinch the ticket of the ruling party with much desire to take over from his principal, President Muhammadu Buhari at the end of his tenur...

Gwamnatin Buhari Ta Ce Za Ta Samar Da Hanyar Saukar Da Farashin Abinci

Ministar kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ta ce gwamnatin tarayya ta fara lalubo zaren kawo karshen matsalar hauhawar farashin abinci a Najeriya. Ministar ta ce za a fito da wata hanyar yin taron kasa da masu ruwa da tsaki domin samar da matakin da za a dogara gare shi wajen rage ma 'yan kasa radadi cikin gaggawa. Idan ana iya tunawa gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kulle kan iyakokin kasar da zimmar bunkasa noma abinda ya haifar da tsananin tsadar abinci.

PDP Na Son Sake Zaben Fidda Gwani A Jahar Bauchi

Rahotanin da ke shigowa yanzu haka na cewa an samu rabuwar kai tsakanin manyan shugabannin jam'iyyar PDP a jahar Bauchi in da jam’iyar ke shirin sake zaben fidda gwanin dan takarar gwamna a jahar. Wannan ya biyo bayan matakin da  Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Kashim ya dauka ne, da ya kekasa kasa ya ce ba zai bai wa gwamna Bala Abdulkadir Muhammad, wanda ya fadi zaben neman takarar shugaban kasa da aka yi a ranar Lahadi ba. Jaridar Daily Trust da DW Hausa duka sun ruwaito wannan labari.

Abubakar Gada Da Salame Sun Janye Daga Zaben Fidda Gwanin APC A Sokoto

Sanata Abubakar Gada da Abdullahi Balarabe Salame sun fitar da sanarwar janyewa daga zaben fitar da gwani na gwamna a jahar Sokoto bayan wata takaddama da ta biyo baya. Takardar da suka fitar ta bayyana cewa tun farko sun nemi a yi zaben ta hanyar 'yar tinke, amma kuma wani bangare na jam'iyyar ya yi watsi da wannan. Sun ce ganin ba za a yi mu su adalci ba ya sa ba za su shiga zaben ba, kuma suna kira ga uwar jam'iyyar APC ta kasa da ta duba yuwar bin bukatar da suka nema tun da farko. A cewar takardar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana cewa duk zaben da aka yi ba tare da amfani da masu zaben 'yan takara da aka fi sani da delegate, ko kuma ta hanyar sulhuntawa ba to haramtacce ne. Kan haka suke neman uwar jam'iyyar da ta san dacewa ba a yi zabe a jahar Sokoto ba, kuma wannan zai iya jawo jam'iyyar APC ta rasa dan takara, in ji su.

Zabar Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jahar Sokoto A Jam'iyyar PDP Ya Bar Baya Da Kura

Bayan da gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci zaman sulhu domin tsayar da dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP tare da zabar Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma, hakan ya haifar da cece-kuce tsakanin jama'a. Daga cikin jerin 'yan takarar da suka nemi kujerar akwai mataimakin gwamnan jahar Sokoto, Alhaji Maniru Muhammed Daniya da kwamishin muhalli na jahar Sokoto, Alhaji Sagir Attahiru Bafarawa da tsohon sakataren gwamnatin jahar Sokoto, Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma da kuma tsohon mataimakin gwamnan jahar Sokoto Alhaji Muktari Shagari. Bayan zama da gwaman Aminu Waziri Tambuwal ya yi da dukan su a dakin taro na kasa da kasa da ke Kasarawa, daga karshe gwamnan ya tabbatar da Sa'idu Umar Ubandoma a matsayin wanda zai yi ma jam'iyyar PDP takarar gwamna a 2023. Rahotannin da ke shigo muna yanzu haka sun tabbatar da cewa shi ma daya daga 'yan takarar da bai yi nasara ba, Alhaji Muntari Shagari ya fice daga jam'iyar ta PDP sai d...

Gwamnatin Jahar Sokoto Ta Sanya Dokar Hana Yawo Tsawon Sa'a 24

Gwamnatin jahar Sokoto ta bayar da sanarwar saka dokar hana yawo a birnin Sokoto da wasu sassan jahar na tsawon sa'a 24. Ofishin mai ba gwamna shawara akan lamurran watsa labarai ne ya fitar da wannan sanarwa ranar asabar 14/05/2022. A cewar sanarwar, an dauki matakin ne don samar da zaman lafiya a jahar. Wannan nan dai na zuwa ne lokacin wata sabuwar zanga-zanga ta barke a birnin na Sokoto, wanda ke da nasaba da kamen da 'yan sanda suka yi na mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan Debirah Samuel Yakubu a Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari kwana biyu da suka gabata. In da da farko zanga-zangar da aka soma ta lumana ta rikide zuwa kone-kone. In da masu zanga-zangar suka cika harabar Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III.

An Kashe Wata Daliba Da Aka Zarga Da Batanci Ga Manzon Allah A Jahar Sokoto

Wata dalibar Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, mai suna Debora Samuel, ta gamu da ajalinta lokacin da wasu matasa da ba a kai ga sanin ko su wanene ba suka kashe ta hanyar kona ta, bayan da aka zarge ta da yin batanci ga Annabi mai tsira da amincin Allah. Lamarin ya kazance ne bayan da wasu daga daliban kwalejin suka yi zargin cewa ta dade ta na wannan batancin abinda ya kai ga barkewar rikicin da ya kai ga salwantar ranta. Tuni dai mahukuntan jahar Sokoto suka bayar da sanarwar rufe kwalejin har a kammala bincike. Babban sakatare a ma'aikatar ilmi mai zurfi ta jahar Sokoto Alhaji Almustapha Usman Ali, ya shaidawa manema labarai cewa, an bayar da umurnin rufe kwalejin kazalika za su sanar da jama'a mataki na gaba idan har an kammala bincike. An dai girke jami'an tsaro a harabar makarantar domin dakile rikicin da ka iya tasowa. Tuni dai da hotunan bidiyo da Tantabara ba ta kai ga tantantace sahihancinsu ba, suka karade shafukan sada zumunta, wadanda k...

Daliban Jahar Sokoto Ba Zasu Rubuta Jarabawar WAEC Ba

Hukumar Shirya Jarabawar Sakandire ta Afirka ta Yamma wato WAEC, ta bayyana cewa jahohin Sokoto da Zamfara ba su aike mata da sunayen dalibansu da za su rubuta jarabbawar kammala babbar sakandire ba, wadda za a soma tsakanin ranakun 16 zuwa 23 ga watan Yunin gobe, kamar yadda sakataren hukumar shirya jarabawar Mista Patrick Aregan ya fitar da sanarwa. Sai dai a hirarsa da Sashen Hausa na BBC, kwamishinan ilmi na jahar Sokoto Bello Abubakar Guiwa, ya ce matsalar ba daga gare su ba ne.  Kwamishinan ya ce hukumar ta WAEC ta fito ne da wani tsari na sun amsar kudi ba gaira ba dalili gare su wanda ya sa suka yi watsi da ita. Ya kara da cewa suna da dalibai kusan 30,000 da zasu rubuta jarabawa a wannan shekara, to amma sai hukumar hana su lambobin jarabawar da ake rabawa dalibai ta kuma ce duk wani kuskure daya da aka samu akan kowane dalibi, wajibi ne sai an biya naira 5000, wanda kuma miliyoyin kudade ne, kazalika sai gwamnatin jahar Sokoto ta biya kashi 40 cikin dari kafin...