Skip to main content

Posts

An Ga Watan Ramadan A Najeriya

An samu ganin jinjirin watan Ramadan a Najeriya a yau kamar yadda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar na Uku ya bayar da sanarwa. An ga watan a jahohin Sokoto da Kano da Katsina da Filato da Adamawa da sauran jahohi n Najeriya. Gobe asabar 2 ga watan Afirilu 2022 za ta zama 2 ga watan Ramadan 1443.

An Ga Watan Ramadan A Saudiyya

An ga jinjirin watan Ramadan a wurare da dama a kasar Saudiyya. Gobe asabar 2 ga Afrilu 2022 za ta zama 1 ga watan Ramadan 1443.

Zamu Yaki 'Yanta'adda Da Kanmu - El-Rufa'i

Cikin hushi gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i ya bayyana cewa idan gwamnatin tarayya ta kasa kare al'umma daga harin 'yan bindiga to fa za su hada kai su kare jama'arsu, ko da kuwa ta kama su dauko sojojin haya daga ketare. Ya fadi hakan a wata hira da BBC ta yi da shi, in da ya ce dukan hare-haren da ake kai wa jama'a gamnatin tarayya na sane kuma sun san mazaunar 'yan ta'addan. Ya kara da cewa da jimawa shi kan sa ya sha ba shugaban kasa shawara akan matakan da ya kamata a dauka na yakar masu tayar da tarzoma da kisan jama'a a jahohin arewa maso gabas da arewa maso yamma amma sai a ka yi biris da shawarar da ya bayar.

Kwankwaso Ya Fice Daga PDP

Getty images Labarin da ke shigo muna yanzu haka sun tabbatar da tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fitar da sanarwar ficewa daga jam'iyyar ta PDP zuwa sabuwar jam'iyyar NNPP, jim kadan bayan da kotu ta bayar da umurnin dakatar da helkwatar jam'iyyar PDP ta kasa daga rusa membobin kwamitin zartaswar jam'iyyar reshen jahar Kano.

An Zabi Abdullahi Adamu Shugaban Jam'iyyar APC

Getty images Jam'iyyar APC ta cimma matsayar zabar tsohon gwamnan jahar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Adamu, a matsayin sabon shugabanta. Kimanin 'yan takara shida ne suka janye daga neman mukamin, da suka hada da tsohon gwamnan jahar Nasarawa Alhaji Tanko Almakura da tsohon gwamnan jahar Borno Ali Modou Sheriff da tsohon gwamnan jahar Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar Mafara da sauran su. Tun da farko dai an bayyana Abdullahi Adamu a matsayin dan takarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke marawa baya.

Sabon Rikici: Bangaren Abdul'aziz Yari Ya Aike Ma Buhari Sako Mai Zafi

A wani abinda ake ganin bai rasa nasaba da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nace akan samar da maslaha a zaben shugaban jam'iyyar APC na kasa maimakon gudanar da zabe, ya sa bangaren Abdul'aziz Yari, tsohon gwamnan jahar Zamfara ya fito fili yana Allah wa dai da matakin shugaban kasa. Yanzu haka jam'iyyar APC na ci gaba da gudanar da babban taronta na kasa a Abuja. Ku latsa hoton da ke kasa don sauraren kalaman bangaren na masu goyon bayan Yari:

An Hana Masu Mukaman Siyasa Jefa Kuri'a A Babban Taron APC Na Kasa

Kwamitin tsare-tsare na musamman na riko na jam’iyyar APC ya kori masu rike da mukaman siyasa daga kada kuri’a a babban taron kasa na ranar Asabar. A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana karara cewa “dukkan wadanda aka nada a siyasance da aka zaba a matsayin wakilai a babban taron kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 26/3/2022, ba za su kada kuri’a ba bisa la’akari da cece-kucen da ke tattare da sashe na 84 (12) na dokar zabe.  2022." KUNA IYA KARANTA:  https://tantabaranews.blogspot.com/2022/03/dole-mai-son-tsayawa-takara-ya-sauka.html Komitin, duk da haka, ya bayyana cewa masu nadin siyasa na iya halarta a matsayin masu sa ido kawai amma kada su dada kada su rage. Hakan ya biyo bayan amincewar da Majalisar Dokoki ta kasa baki daya ta yi da dokar gyaran dokar zabe da shugaban kasa Muhammadu ya sanya wa hannu Alamu sun bayyana a ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa da gwamnonin jam’iyyar APC suka amince da batun fitowar jami’an...

Kotu Ta Tabbatar Da Isah Sadik Achida Matsayin Shugaban Jam'iyyar APC Na Jahar Sokoto

Babbar kotun daukaka kara ta kasa mai mazauninta a Abuja ta tabbatar da Alhaji Isah Sadik Achida a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jahar Sokoto. An dai shafe wata daya ana jayayya a kotu tsakanin Alhaji Isah Sadik Achida da bangaren Mainasara Abubakar da ke tare da Alhaji Abdullahi Salame sai kuma bangaren shugaban majalisar dokoki ta jahar Sokoto Hon. Aminu Manya Achida. Idan ana iya tunawa dai babban mai saka kara na kasa kuma ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami SAN, ya taba wani ikirari na cewa kotu za ta tabbatar da shugabancin ga Mainasara Abubakar da ke bangaren Hon. Abdullahi Salame, wanda wannan hukuncin ya zama tamkar watsa kasa a fuskar ministan shari'ar da ya yi riga malam masallaci gabanin hukuncin kotu.

Sabuwar Dambarwar Shugabancin APC

Kwana biyu kafin ta gudanar da babban zabenta na kasa, jam'iyyar APC ta sake tsunduma wata sabuwar turka-turka game da makomar wanda za a zaba matsayin sabon shugabanta. A wata hira da BBC Hausa, gwamnan jahar Kebbi Abubakar Atiku Bagudo, wanda kuma shi ne shugaban gwamnonin APC na kasa ya ce yanzu haka sun kasa cimma matsaya akan wanda zai zama shugaban jam'iyyar a ranar asabar mai zuwa. Bagudo ya kara da cewa sun gana da shugaba Muhammadu Buhari akan samar da matsaya, amma kuma sun lura cewa da wuya idan ba zabe za a gudanar ba a maimakon samar da maslaha. Da aka tambai shi ba ya ganin samar da maslaha tamkar an tilastawa wani ne bin abinda ba ya so, shugabana kungiyar gwamnonin ya ce zai yuwu a sulhunta amma idan hakan ta gagara za a bi hanyar da za ta kawo mafita. Sai dai bai yi cikakken bayani akan wace hanya ce da za a bi idan har an kasa yin sulhu tsakanin 'yan takara. Ga alama wannan na nuna irin yadda jam'iyyar za ta fuskanci kalubale gabanin ko ba...

An Tilas Ni Tsayawa Takara - In Ji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana bukatar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a karo na biyar, in da ya ce ya wajaba ne ya karba kiran jama'a. Atiku ya yi wannan magana ne a birnin tarayya Abuja lokacin da ya ke sanar da muradin nasa, "Abubuwan da suka ja hankalina na da yawa, muhimmai daga cikin su akwai bukatar samar da hadin kai, tsaro da tattalin arziki, ciyar da bangarorin gwamnatin tarayya gaba da sauran su". Atiku Abubakar na bayyana wannan ne daidai lokacin da gwamnan jahar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa Aminu Waziri Tambuwal shi ma ya bayyana anniyarsa ta tsayawa neman shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar ta PDP. Tambuwal ya ce babu wani da ya fi dacewa ya mulki kasar nan a wannan lokaci da ake ciki idan ba shi ba. Ya bayyana kan sa a matsayin matashi kuma wanda ya goge a harkar siyasa masanin dubarun mulki da ya san makomar Najeriya...