Cikin hushi gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i ya bayyana cewa idan gwamnatin tarayya ta kasa kare al'umma daga harin 'yan bindiga to fa za su hada kai su kare jama'arsu, ko da kuwa ta kama su dauko sojojin haya daga ketare.
Ya fadi hakan a wata hira da BBC ta yi da shi, in da ya ce dukan hare-haren da ake kai wa jama'a gamnatin tarayya na sane kuma sun san mazaunar 'yan ta'addan. Ya kara da cewa da jimawa shi kan sa ya sha ba shugaban kasa shawara akan matakan da ya kamata a dauka na yakar masu tayar da tarzoma da kisan jama'a a jahohin arewa maso gabas da arewa maso yamma amma sai a ka yi biris da shawarar da ya bayar.
Comments