Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kabi ta tabbatar da sace wata yarinya‘ yar shekaru 18 (da aka sakaya sunanta) a Gangaren NEPA, Birnin Kabi, babban birnin jihar Kebbi a farkon safiyar yau Juma’a. DSP Nafi’u Abubakar, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Birnin Kabi. Ya ce jami'a 'yan sanda sun yi duk mai yiwuwa don ceto yarinyar amma abin ya faskara Abubakar ya shawarci jama'a da akoyaushe su dinga kai rahoton duk abinda ba su amince da shi ba, domin hakan zai taimaka wajen yakar ayukkan ta'addanci. An kuma gano cewa mahaifin yarinyar da aka sace, Faruq Mohammed jami'in Hukumar Tsaro ta (NSCDC), ta Jihar Kabi ne. Da yake magana a wata hira da manema labarai, Mohammed, ya ce ‘yan bindigar sun shigo unguwar ne kwaram “Lokacin da suka zo gidana, na lura tare da jiro hayaniya kuma na fahimci cewa wani abu da ba daidai ba da ke shirin aukuwa. “Ina da hanyoyi biyu a gidana: daya a gaba yayin da kuma dayar ke cikin gar...