Shugabar Hukumar kula da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM) Abike Dabiri-Erewa, ta yaba wa Babban Bankin Najeriya (CBN) kan bullo da shirin.
A wata sanarwa da jami'in hulda da jama’a na NIDCOM, Abdur-Rahman Balogun ya sanya wa hannu, Dabiri-Erewa ta ce shirin wani abin ci gaba ne da aka yi maraba da shi, domin zai karfafawa maziyarta damar aika kudi ta hanyoyin hukuma.
Shi ma bankin na CBN, ya bayyana cewa wannan tsari wani kwarin gwiwa da ci gaba ne ga masu musayar kudaden kasashen waje inda masu aiko da kudaden zasu biya naira 5 a kan kowace dala da aka ka shigo da ita.
Dabirewa ta ce manufar idan aka aiwatar da ita yadda ya kamata, za ta yi tasiri ga tattalin arzikin Najeriya.
Ta ce yanzu haka ofishin hulda da 'yan Najeriya mazauna kasashen wajen na kan samar da wani asusun na musamman ta yadda ‘yan Nijeriya mazauna kasashen wajen za su iya tsarawa da kuma gabatar da jarin su, da sauran lamurran da suka shafi hada-hadar kudi.
Babban bankin na CBN ya yi bayanin cewa ana sa ran wannan sabuwar manufar za ta jawo hankulan mazuna kasashen ketare ta hanyar sanya kudadensu a inda ya dace, zai kuma yi matukar tallafawa tattalin arzikin Najeriya.
Comments