Rundunar āyan sanda reshen jihar Kabi ta tabbatar da sace wata yarinyaā yar shekaru 18 (da aka sakaya sunanta) a Gangaren NEPA, Birnin Kabi, babban birnin jihar Kebbi a farkon safiyar yau Jumaāa.
DSP Nafiāu Abubakar, jamiāin hulda da jamaāa na āyan sanda, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Birnin Kabi.
Ya ce jami'a 'yan sanda sun yi duk mai yiwuwa don ceto yarinyar amma abin ya faskara
Abubakar ya shawarci jama'a da akoyaushe su dinga kai rahoton duk abinda ba su amince da shi ba, domin hakan zai taimaka wajen yakar ayukkan ta'addanci.
An kuma gano cewa mahaifin yarinyar da aka sace, Faruq Mohammed jami'in Hukumar Tsaro ta (NSCDC), ta Jihar Kabi ne.
Da yake magana a wata hira da manema labarai, Mohammed, ya ce āyan bindigar sun shigo unguwar ne kwaram
āLokacin da suka zo gidana, na lura tare da jiro hayaniya kuma na fahimci cewa wani abu da ba daidai ba da ke shirin aukuwa.
āIna da hanyoyi biyu a gidana: daya a gaba yayin da kuma dayar ke cikin gareji.
āNa yanke shawarar cewa ya kamata mu fita ta cikin gareji; cikin rashin sa'a, da bude kofar, sai muka hadu da daya daga cikin 'yan fashin dauke da muggan makamai a gefen motata, cikin hanzari muka nemi wata hanya sannan muka tsallaka zuwa gidan makwabta.
āYan fashin sun kutsa cikin gida na suka fara bincike daki daki. abin takaici, āyata tana kwance a dakinta, lokacin da suka kwankwasa ta bude dakin sai suka dauke ta suka tafi da ita.ā
Wata majiya mai tushe ta ce 'yan fashin sun kuma kai hari gidan wani Malam Sanusi Nagoru wanda ya yi jaruntakar tare da biyu daga cikin 'yan ta'addan kuma ya fi karfin su, ya kara da cewa mutumin ya nemi taimako daga wasu mutane.
Majiyar ta ce, babu wanda ya ba shi goyon baya don fatattakar 'yan bindigar, ta kara da cewa ba shi da wani zabi da ya wuce ya gudu da ransa.
āDa ya ga wasuā yan fashi sun zo su taimaka musu, sai mutumin ya ture ya ture wadannan āyan fashin, ya ranta a na kare.
Daya daga cikin matansa ta zo ta toshe kofar don ta hana barayin shiga babbar hanyar shiga.
Majiyar ta kara da cewa, ''Gani hakan ya sa suka bude wuta suka harbe ta a cinya, wacce yanzu haka ke amsar magani a Cibiyar Kiyon Lafiya Ta Tarayya (FMC) da ke Birnin Kabi."
Comments