Skip to main content

Posts

Biden Ya Nemi Magoya Bayansa Su Tsaya A Gida Lokacin Rantsar Da Shi

A daidai lokacin da ake daf da rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden, an baza dubban jami'an tsaron soji domin murkushe duk wata zanga-zanga da ka iya barkewa. Tun a farkon makon da ya gabata ne dai Hukumar Leken Asiri ta Amurka ta FBI, ta yi gargadin cewa akwai yuwar samun tarzoma a ko'ina a kasar. Zababben shugaban dai ya shawarci jama'a da su yi zaman su a gida ba sai sun halarci bukin rantsarwar ba, ko baya ga matsalar annobar korona akwai yuwar dakarun sojin da aka baza na shirin maganin duk wanda ya nemi daukar dala ba gammo. Shugaba Donald Trump mai barin gado ya bayyana cewa zai bar babban birnin kasar Washington DC tun da sanyin safiyar gobe laraba, don kaucewa yin ido biyu da wanda zai gaje shi. A tarihin kasar dai wannan ne karon farko da za a yi bukin rantsarwa mafi tsaurin tsaro a Amurka, da kuma armashinsa ya ragu, muddin ta tabbata bai samu halarcin jama'a ba.

Akwai Yuwar Sake Rufe Makarantu A Nijeriya Saboda Korona

A irin yadda cutar korona ke ci gaba da kamari a duniya, mai yuwa kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar na shirin bayar da shawara don sake kulle makarantu da zaran aka ga alkalumman masu kamuwa da ita na ci gaba da karuwa. An dai bude makarantun ne a ranar 18 ga wannan wata na Janairu, koda ya ke gwamnonin jahohin Kaduna da Edo ba su amince da bude makarantun ba. Ministan Ilmi Malam Adamu Adamu da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha sun gana da shuwagabannin kwamitin yaki da annobar korona don daukar mataki na gaba, da ake jin bai rasa alaka da sake rufe makarantun. Bayan bude makarantu a jiya, galibin al'ummar kasar sun yi suka akan matakin, da suka ce mai hadarin gaske ne saboda abu ne mai wuya hukumomin makarantu a Najeriya su iya cika ka'idojin da aka gindaya, kasancewar ajujuwa a makarantun makare suke da dalibai da zai yi wahala a bada tazara tsakani.

Wasu Daga Hotunan Gobarar Kasuwar Sokoto

DA DUMI DUMI Gobara Ta Kama A Babbar Kasuwar Sokoto

Tun da sanyin safiyar yau gobarar ta tashi a bangaren masu kayan robobi da ke Babbar Kasuwar Jahar Sokoto, abinda ya haddasa hasarar dukiyar da ba a kai ga gano adadinta ba a halin yanzu. Babbar matsalar da ake fuskanta ita ce rashin hanyar da motocin kashe gobara za su bi, wanda wannan ya kara hayyaka matsalar gobarar da ke ci gaba da yaduwa zuwa wasu sassan kasuwar. Wannan ya sa masu dukiyar da ke ci gaba da konewa rashin sanin madogara, face diban kayansu da hannuwa ko don tsira da wani abu. Wasu da TANTABARA ta samu zantawa da su, sun bayyana cewa su kam sun tafka hasara, domin karfin wutar ba zai bar su fitar da wasu muhimamman abubuwa ba. To sai dai babu wani rahoton jikkata ko rasa rai kawo yanzu, wanda shi ne abinda ake fata.

Da Dumi Dumi - An Tsige Shugaba Trump

Majalisar wakilan Amurka sun samu yawan kuri'un da za su kai ga tsige shugaba Donald Trump. Wannan ya tabbatar da shi a matsayin shugaban Amurka na farko da ka tsige har sau biyu. Kuma wannan zai hana ma sa sake rike kowane irin mukamin siyasar kasar nan gaba da kuma bada damar gurfanar da shi don fuskantar tuhuma a gaban kotu. Ga jerin shuwagabannin Amurka da aka taba tsigewa:  A shekarar 1868 an tsige shugaban Amurka Andrew Johnson,  Sai kuma shugaba Bill Clinton da aka taba tsigewa a 1998. Bayan sa kuma sai shugaban Amurka mai barin gado Donald J. Trump shi kuma  a 2019. Bayan nan kuma yau 13 ga watan Janairun 2021 an sake tsige tsohon shugaban a karo na biyu.

An Soma Jefa Kuri'ar Tsige Trump

'Yan majalisar wakilan Amurka yanzu haka sun soma jefa kuri'ar tsige shugaba Donald J. Trump. Sun soma kada kuri'ar ne bayan kammala muhawarar da ta bada damar ci gaba da daukar mataki na gaba, wanda shi ne kada kuri'ar amincewa ko akasin haka. An dai baza dubban jami'an tsaron soji a ko'ina ciki da harabar majalisar dokoki ta Capitol Hill don shirin ko ta kwana. Bayan kammala jefa kuri'ar daga baya za a turawa majalisar dattijai don daukan mataki na gaba da zai iya kai ga tsige shi ko sabanin haka. Idan har haka ta tabbata zai zama kenan Trump shi ne shugaban Amurka na farko a tarihi da aka tsige har sau biyu. Wannan sabon matakin na da nasaba da jawaban shugaban a makon jiya, da 'yan majalisar suka ce sun kai ga tunzura magoya bayansa har suka kai wa majalisar hari da yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyar, ciki kuwa har da jami'in dan sanda da ke kare masu zanga-zangar daga kutsa kai ginin majalisar.

Matsalar Tsaro Ta Addabi Jahar Sokoto

A daren jiya Talata ne wasu yan bindiga sukayi dirar mikiya a wani kauye mai suna Chacho da ke karamar hukumar mulki ta Wurno da ke jahar Sokoto. Rahotanni na cewa maharan sun kai wa wani Dan kasuwa mai suna Alhaji Jamilu samame ne da niyyar hallaka shi, amma da hakansu ba ta cimma ruwa ba suka yi awon gaba da mahaifinsa hadi da matarsa da kuma harbin kanensa, tare da karbar kudin da suke mallakarsa ne kimanin naira dubu dari shida da sittin. Maharan sun kuma harbe wani dan banga har lahira, mai suna Malam Rabi'u. Wannan lamarin yawitar hare-hare a jahar Sokoto na neman gagarar kundila, domin kwana daya kawai kafin wannan harin wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a wani gari da ke karamar hukumar ta Wurno da suka karbi kudi naira miliyan daya daga hannun wani dan kasuwa kafin daga bisani jami'an tsaro su yi nasarar kama biyar daga cikin su.

DA DUMI-DUMI 'Yan Majalisar Amurka Sun Soma Zama Don Tsige Trump

'Yan majalisar dokokin Amurka sun soma wani zama na musamman yanzu haka, don shirin tsige shugaba Donald Trump, ana sauran kwanaki 9 kacal a rantsar da zababben shugaban kasar Joe Biden. Kakakin majalisar dattawan kasar Nancy Pelosi a wata hira da tashar talabijin ta NBC, ta ce, "Mista Trump zai fuskanci zahiri ta hanyar girbar abinda ya shuka". Ta ce za su nemi mataimakinsa Mike Pence ya aminta tare da sa hannu akan kudurin dokar da zai nuna amincewa da cewa shugaba Trump bai dace ya shugabanci kasar ba, ko kuma idan har hakan ta ci tura, su soma jefa kuri'ar amincewa da tsige shi a tsakiyar makon nan. Idan har hakan ta tabbata wannan ya nuna Trump ne shugaban Amurka na farko da aka taba tsigewa har sau biyu. Kuma hakan zai bata ma sa suna da makomar siyasa nan gaba. Masana shari'a na ganin bayan tsige shi, zai iya fuskantar tuhuma akan zargin ingiza magoya bayansa su kai hari da zanga-zanga a majalisar dokokin kasar, domin hana amincewa da zaben Joe ...

Kwalejin Ilmi Ta Sokoto Za Ta Koma Jami'ar Ilmi Ta Sokoto - Tambuwal

Gwanan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya lashi takobin ganin kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari ta koma Jami'ar Horas da Malamai da Fannonin Ilmi Ta Jahar Sokoto. Ya fadi hakan yau litinin a lokacin bukin cikar kwalejin shekaru 50 da kafuwa, karo na 22. Ya yi karin hasken cewa ganin yadda ya dauki sha'anin ilmi da muhimmanci da ma yadda ya ke ware masa kaso mafi tsoka a kasafin kudin gwamnatinsa, zai gana da masu ruwa da tsaki a fannin ilmi da ma mai alfarma Sarkin musulmi don neman shawara akan wannan batu. Ya kara da cewa zai kara ginawa kwalejin karin dakunan kwanan dalibai, domin saukake matsalar cin koso. To amma kuma, wasu da TANTABARA ta zanta da su, na kallon batun a matsayin irin alkawurran  da ya ta bayi na samar da karin Sassan nazarin ilmin kimiyya da liktanci a Jami'ar Jahar Sokoto,  tun shekaru uku da suka gabata, amma suka zama durmukyal da suka ce kalamai ne na rufa ido kawai da ya saba da su. To, sai dai aikin gina asibitin koyarwar jami'ar ...

An Rufe Makarantu Da Wuraren Holewa A Najeriya

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Boss Mustapha ne ya bayar da umurnin a jiya, cewa dukan makarantu da wuraren shakatawa za su kasance a rufe har tsawon makonni biyar. Gwamnatin ta kuma bayar da umurnin ma'aikata daga mataki na 12 zuwa kasa su yi zaman su a gida, in ban da ma su aikin gaggawa, kamar jami'an kiyon lafiya da sauran su. Wannan matakin ya biyo bayan yadda annobar korona ke ci gaba da hayyaka a Najeriya. Haka ma an jiyo ministan lafiyar kasar Osagie Ehanire na bayar da umurnin sake bude cibiyoyin killace wadanda suka kamu da cutar. Tuni dai wasu jahohin kasar da suka hada da Legas, Kaduna da Imo suka bayar da damar rufe makarantu tare da gindaya dokoki da ka'idojin yaki da cutar, ta hanyar rufe wuraren rawa da takaita zirga-zirga da kayyade lokacin halartar wuraren ibada da ma saka takunkumi.