Skip to main content

Kwalejin Ilmi Ta Sokoto Za Ta Koma Jami'ar Ilmi Ta Sokoto - Tambuwal

Gwanan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya lashi takobin ganin kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari ta koma Jami'ar Horas da Malamai da Fannonin Ilmi Ta Jahar Sokoto.
Ya fadi hakan yau litinin a lokacin bukin cikar kwalejin shekaru 50 da kafuwa, karo na 22.
Ya yi karin hasken cewa ganin yadda ya dauki sha'anin ilmi da muhimmanci da ma yadda ya ke ware masa kaso mafi tsoka a kasafin kudin gwamnatinsa, zai gana da masu ruwa da tsaki a fannin ilmi da ma mai alfarma Sarkin musulmi don neman shawara akan wannan batu.
Ya kara da cewa zai kara ginawa kwalejin karin dakunan kwanan dalibai, domin saukake matsalar cin koso.
To amma kuma, wasu da TANTABARA ta zanta da su, na kallon batun a matsayin irin alkawurran  da ya ta bayi na samar da karin Sassan nazarin ilmin kimiyya da liktanci a Jami'ar Jahar Sokoto,  tun shekaru uku da suka gabata, amma suka zama durmukyal da suka ce kalamai ne na rufa ido kawai da ya saba da su.
To, sai dai aikin gina asibitin koyarwar jami'ar da ke ci gaba da yi yanzu haka, na nuna alamun share hanya ga alkawarin da gwamnatin jahar ta Sokoto ta dauka a wancan lokaci.
Yanzu dai lokaci ne zai tabbatar da wannan batu sabo.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey