Skip to main content

An Rufe Makarantu Da Wuraren Holewa A Najeriya

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Boss Mustapha ne ya bayar da umurnin a jiya, cewa dukan makarantu da wuraren shakatawa za su kasance a rufe har tsawon makonni biyar.
Gwamnatin ta kuma bayar da umurnin ma'aikata daga mataki na 12 zuwa kasa su yi zaman su a gida, in ban da ma su aikin gaggawa, kamar jami'an kiyon lafiya da sauran su.
Wannan matakin ya biyo bayan yadda annobar korona ke ci gaba da hayyaka a Najeriya.
Haka ma an jiyo ministan lafiyar kasar Osagie Ehanire na bayar da umurnin sake bude cibiyoyin killace wadanda suka kamu da cutar.
Tuni dai wasu jahohin kasar da suka hada da Legas, Kaduna da Imo suka bayar da damar rufe makarantu tare da gindaya dokoki da ka'idojin yaki da cutar, ta hanyar rufe wuraren rawa da takaita zirga-zirga da kayyade lokacin halartar wuraren ibada da ma saka takunkumi.

Comments