A farkon makon nan a ka gano wata nau'in kwayar cutar korona da ta sha bamban da wacce aka sani.
Ita dai wannan sabuwar kwayar cuta ta bulla ne a kasar Burtaniya, in da ta yi nasarar mamaye birnin Landan da gasbascin kasar a yankunan Surrey, Essex, Backshire, Backinghamshire Kent da sauran su.
Firaminstan kasar Boris Johnson ya ce a halin da ake ciki yanzu, kwayar cutar na bazuwa ne cikin sauri fiye da ta farko; wanda yanzu haka ta ke kashi 70 cikin dari a mizanin yaduwa.
Masana kiyon lafiya a duniya sun bayyana cewa, ba Burtaniya kadai wannan sabuwar korona ta bulla ba, har da da Afirka ta kudu da ma sauran sassan duniya kawai dai ba a kai ga farga da hakan ba ne. A cewar su, Burtaniya dai ce ta yi kwakkafin gano ta saboda tsananin bincike da gwajin da ta fi kowace kasa yi kan wannan cuta.
Tuni dai kasashen duniya da suka hada da Jamus, Faransa, Italiya, Austireliya, Iceland, Spaniya, Saudiyya da sauran su, suka dakatar da zirga zirgar jiragen sama tsakaninsu da kasar ta Burtaniya.
Annobar korona dai ta sake dawowa da wata fuska ta daban, in da ko a karshen makon jiya kimanin mutum 27,000 suka kamu da ita a Amurka a rana daya kawai.
Comments