Skip to main content

Posts

Sanwolu Da El-Rufai Sun Killace Kan Su Saboda Covid-19

Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i ya kebe kan sa saboda wani daga cikin iyalinsa da hadimansa sun kamu da cutar korona. Gwamnan ya bayyana hakan a shafinsa na tweeter, in da ya ce a gobe lahadi zai je asibiti don auna shi a tabbatar idan har yana dauke da ita. Shi ma gwamnan jahar Legas, Babajide Sanwolu ya bayyana killace kansa sakamakon samun wasu na kusa da shi dauke da cutar. Sanwolu ya bayyana cewa wajibi ne ya kebe kan sa kafin a gudanar da gwaji, gudun kada idan ya na dauke da ita ya yadawa wasu makusanta. Jahar Legas dai na sahun gaba daga jerin masu dauke da cutar a Najeriya. Duka jahohin biyu sun yi fama da dokar kulle a watannin baya lokacin da annobar ta yi kamari. Kwanaki uku da su ka gabata an jiyo gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i, na barazanar kulle jahar muddin jama'a suka ci gaba da kin bin ka'idojin yaki da cutar korona da aka san da su.

Mutum 64 Sun Kamu Da Korona A Kaduna - El-Rufa'i

Gwamnatin jahar Kaduna ta fitar da sanarwar cewa annobar korona ta sake dawowa a jahar. Gwamnatin jahar ta tabbara da samun sabbin kamuwa da cutar har mutum 64, wanda a cewar ta tuni su ma a ka kebe su. An kuma jiyo gwamnan jahar Malam Nasiru El-Rufa'i, na cewa muddin jama'ar jahar suka ci gaba da yin biris da dokokin da aka shata musu to babu makawa gwamnatin za ta sake kulle su ruf har sai lokacin da annobar Covid-19 din ta lafa. Gwamnan ya ce yana mamakin yadda al'umma ke watsi da ka'idojin da tuni aka san da su, na rage cin koso da sanya takunkumi da kuma yawaita wanke hannuwa. Jahar Kaduna na cikin jahohin da suka fuskanci dokar kulle sakamkon barkewar annobar ta korona a watannin baya. To sai dai wannan gargadi na gwamnatin jahar ya gamu da suka, musamman ga wadanda ke kallon kalaman a matsayin na 'yan boko.

Maina Ya Kife A Kotu

 Tsohon shugaban kwamitin hana badakala a hukumar fansho ta kasa Abdulrasheed Maina, ya fadi a kotun birnin tarayya a Abuja, daidai lokacin da ake tsaka da yi masa shari'a. Tsohon shugaban kwamitin dai ana tuhumar sa ne da badakalar da ta danganci batar da kimanin naira biliyan biyu sa'adda da ya ke jagorancin kwamitin. Tun daga lokacin da aka kai shi kotu Maina ya yi batan dabo bayan da ya samu beli. Bayan kwashe tsawon lokaci ana neman sa daga bisa ni an yi nasarar gano shi a kasar Jamhuriyar Nijar. Wannan al'adar faduwa a gaban kwamitocin bincike ba bakuwa ba ce a Najeriya, in da ko watannin baya shugaban kwamitin Hukumar Raya Yankin Naija Delta (NDDC) farfesa Podei ya yi zaman tsumma a kwando, lokacin da yake amsa bahasi a gaban kwamitin majalisar wakilai na kasa dangane da badakalar da ake zargin sa da hannu na karkata kwangiloli da kudaden hukumar zuwa wata hanya daban.

Kotu Ta Aminta Da Rataye Maryam Sanda

Yau din nan kotun birnin tarayya Abuja ta tabbatar da hukunci da kotun baya ta yanke na rataye Maryam Sanda. Kotun ta bayyana cewa hukuncin da aka yanke ma ta tun da farko babu kuskure cikin sa saboda haka ta bayar da umurnin gaggauta rataye ta. An dai samu Maryam sanda da laifin kashe mijinta har lahira ta hanyar daba masa wuka. Amma ta daukaka kara kan hukuncin da aka yanke ma ta a watan Janairun wannan shekara ta 2020.

Barayi Sun Yiwa Ofishin Jaridar Daily Star Nigeria Kaf

A yau da rana wasu gungun barayi da ba a kai ga ganowa ba sun kai samame ofishin jaridar Daily Star Nigeria da ke jahar Sokoto. Babban editan jaridar, Dr. Mansur Isah Buhari ya tabbatar da wannan lamari, in da ya ce barayin sun yi awon gaba da wasu muhimman kaya da suka hada da kananan kwamfutoci, da akwatin talabijin da ma wasu kudaden da ba a bayyana adadinsu ba kawo yanzu. Dr. Mansur ya ce, "kamar yadda al'adar ofishinmu ta ke, wakilanmu na wajen nemo labarai ni kai na ma na dan fita bana wajen, lokacin da barayin suka auni hakan tare da fasa kofar ofishin in da suka wawushe kome". Jaridar Daily Star Nigeria dai na cikin na gaba gaba daga cikin jerin jaridun yanar gizo da ake da su a Nijeriya yanzu haka.

Kungiyar Boko Haram Ta Dauki Alhakin Kisan Manoma 78 A Jahar Borno

A cikin wani sabon faifan bidiyo da kungiyar ta fitar a yau, shugabanta Abubakar Shikau ya ce su ne suka aikata kisan manoman a garin Zabarbarin jahar Borno. Shikau ya ce sun yi wannan ne saboda fansa game da abinda sojojin Najeriya ke yi musu da taimakon al'umma. In da ya ci gaba da cewa da dama daga mazauna yankunan na tseguntawa jami'an tsaro maboyarsu, wanda hakan kan kai ga kama su. Shugaban kungiyar ya ce, sun dauki matakin yanka duk wanda ya ci gaba da tseguntawa jami'an sojoji sirrinsu. Har kawo yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta mayar da martani kan wannan sabuwar sanarwa da kungiyar Boko Haram ta fitar ba.

Gwamnatin Tambuwal Na Shirin Ba Da Mamaki

Gwamnatin jahar Sokoto ta yunkoro wajen samar da ayukkan raya gari, tun daga soma aikin Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Jahar Sokoto da kuma Makarantar 'Yan Mata da ke garin Kasarawa galibin mazauna jahar ke ganin cewa an soma samun sauyi. Ganin yadda aka soma wasu ayukan da aka yi shekaru ana jira. Kuma cikin sauri da kamala. Tun lokacin zuwan gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal a 2015, galibin jama'a ke fadin albarkacin baki ganin gudanar da ayukkan kamar da wasa. To sai dai kuma, gwamnatin ta bayar da kwangiloli da suka hada da gina gadojin sama guda biyu da aka ce za a gina nan take. Kazalika da samar da filin wasa katafare da aka ambata da sauran su. TANTABARA ta zanta da wasu mazauna yankunan da ake ayukan in da suka shaida mata cewa suna murna da samar da ci gaban idan har ya tabbata. Haka ma wasu da dama sun soma samun hanyar abin kaiwa bakin salati daga soma ayukkan, inda suka kakkafa sana'o'insu a wuraren. A ziyarar da TANTABARA ta kai wura...