Skip to main content

Sanwolu Da El-Rufai Sun Killace Kan Su Saboda Covid-19

Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i ya kebe kan sa saboda wani daga cikin iyalinsa da hadimansa sun kamu da cutar korona.
Gwamnan ya bayyana hakan a shafinsa na tweeter, in da ya ce a gobe lahadi zai je asibiti don auna shi a tabbatar idan har yana dauke da ita.
Shi ma gwamnan jahar Legas, Babajide Sanwolu ya bayyana killace kansa sakamakon samun wasu na kusa da shi dauke da cutar.
Sanwolu ya bayyana cewa wajibi ne ya kebe kan sa kafin a gudanar da gwaji, gudun kada idan ya na dauke da ita ya yadawa wasu makusanta.
Jahar Legas dai na sahun gaba daga jerin masu dauke da cutar a Najeriya. Duka jahohin biyu sun yi fama da dokar kulle a watannin baya lokacin da annobar ta yi kamari.
Kwanaki uku da su ka gabata an jiyo gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i, na barazanar kulle jahar muddin jama'a suka ci gaba da kin bin ka'idojin yaki da cutar korona da aka san da su.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

Binani Na Neman Kotu Ta Tabbatar Da Ita Wadda Ta Lashe Zaɓen Adamawa

Magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Adamawa a ranar Litinin sun fito kan tituna domin nuna adawa da ayyana Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan Adamawa. Sai dai ita Binani ta buƙaci wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) daga sauya matakin da aka ɗauka na ayyana ta da a ka yi a matsayin wadda ta lashe zaɓen.  A wata buƙata da ta shigar a ranar Litinin, mai neman izinin kotun ya nemi izinin kotun ta ba ta damar shigar da buƙatar neman umarnin haramtawa INEC daga ɗaukar duk wani mataki na watsi da sanarwar da aka yi a ranar 16 ga Afrilu da Kwamishinan zaɓen jahar, Barista Hudu Ari ya ayyana ta a matsayin wadda ta samu ƙuri'u mafifi rinjaye kuma ta lashe zaɓen alhali ba a kammala tattara sakamakon zaɓen gaba ɗaya ba. Ta kuma nemi a ba da umarnin hana hukumar zabe ta INEC, da wakilinta nadawa ko kuma duk wanda ke wakiltarta daukar wasu matakai na bayyana wanda ya lashe zaben gwamna da ak...