Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya shigar da ƙara domin hana wani sabon yunƙurin jam’iyyar PDP dakatar da shi daga cikinta, kuma ya buƙaci kotun da ta ɗauki mataki ga duk masu wannan aniya. Ɗaya daga cikin jigajigan jam'iyyar PDP da suka mayar da martani kan ƙarar da gwamna Wike ya shigar, Mahdi Shehu, ya mayar da martani a ranar Litinin da ta gabata inda ya wallafa a shafinsa na twitter wata sanarwa cewa, “Wike ya shigar da ƙara kan jam’iyyar PDP mai lamba FHC/ABJ/CS/139/2023 ta hannun lauyoyinsa, DY Musa (SAN); Douglas Moru, da C. C. Chibuike, yana neman a ba shi umarnin hana a kore shi daga PDP.” Wike dai ya yi ta famar ruguza jam’iyyar har ma ya rasa inda za shi. Gwamnan na Ribas ya zamewa jam'iyyar PDP ƙadangaren bakin tulu, irin yadda ya ke uwa da makarbiya tun bayan da dangantaka ta soma tsami tsakaninsa da wasu jigajigan jam'iyyar ciki kuwa har da gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.