Dazu dazun nan gwamnatin jahar Kanon ta tura jami'an ma'aikatar lura da tsarin filaye in da ta ruguza makarantar Malam Abduljabbar. Gwamnatin dai ta taba bayyana cewa filin da ya ke amfani da shi haramtacce ne, in da ta kai ga kwace shi tare da bada umurnin gudanar da wasu muhimman ayukka a wurin. Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin gwamnatin jahar Kano da Abduljabbar in da a ranar laraba sakataren watsa labaran gwamnatin jahar, Muhammad Garba ya bayar da sanarwar rufe masallacin Malam Abduljabbar tare da hana masa gudanar da wa'azi baki daya. In da ta ce hakan na da alaka da irin yadda ya ke tunzura jama'a a kalaman da ya ke amfani da su a lokacin da ya ke da'awa.