Skip to main content

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Abduljabbar Nasir Kabara Daga Yin Wa'azi, Ta Rufe Masallacinsa

Malamin nan da aka fi sani da ra'ayi na daban da ke tsaka-tsakin mashabar Shi'a da Darika da ya ke da'awar cewa yake bi.
Ya dai hadu da hushin gwamnatin jahar Kano sakamakon kalamansa da gwamnatin ta bayyana da cewa za su iya haddasa fitina a jahar.
Abduljabbar Kabara dai sananne ne a kafofin sada zumunta da kuma shafukan YouTube in da ya ke watsa kalamansa da bincike ya tabbatar da sun fi karkata wajen zagin sahabbai, abinda kuma galibin jama'a da malamai suka ce ra'ayi ne irin na Shi'a.
Gwamnatin dai ta bakin kwamishinan watsa labaran jahar Muhammad Garba, ta tabbatar da wannan umurnin. Ya kuma kara da cewa an ba kwamishin 'yan sandan jahar umurni da nan take ya tabbatar da an rufe masallacinsa mai suna As-habul Kaf da ke unguwar Gwale, a tsakiyar birnin Kano, tare da bayar da umurnin hana masa duk wani abu da ya kira wa'azi.
Sai dai yayin da wannan umurnin ya zo a daren laraba, wasu na ganin batun bai rasa alaka da siyasa, to amma kuma an dade jama'a na Allah wadai akan kyale shi da aka yi yana kalaman rashin mutuntawa da neman muhawara ba gaira ba dalili.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey