Skip to main content

Posts

Zabar Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jahar Sokoto A Jam'iyyar PDP Ya Bar Baya Da Kura

Bayan da gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci zaman sulhu domin tsayar da dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP tare da zabar Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma, hakan ya haifar da cece-kuce tsakanin jama'a. Daga cikin jerin 'yan takarar da suka nemi kujerar akwai mataimakin gwamnan jahar Sokoto, Alhaji Maniru Muhammed Daniya da kwamishin muhalli na jahar Sokoto, Alhaji Sagir Attahiru Bafarawa da tsohon sakataren gwamnatin jahar Sokoto, Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma da kuma tsohon mataimakin gwamnan jahar Sokoto Alhaji Muktari Shagari. Bayan zama da gwaman Aminu Waziri Tambuwal ya yi da dukan su a dakin taro na kasa da kasa da ke Kasarawa, daga karshe gwamnan ya tabbatar da Sa'idu Umar Ubandoma a matsayin wanda zai yi ma jam'iyyar PDP takarar gwamna a 2023. Rahotannin da ke shigo muna yanzu haka sun tabbatar da cewa shi ma daya daga 'yan takarar da bai yi nasara ba, Alhaji Muntari Shagari ya fice daga jam'iyar ta PDP sai d...

Gwamnatin Jahar Sokoto Ta Sanya Dokar Hana Yawo Tsawon Sa'a 24

Gwamnatin jahar Sokoto ta bayar da sanarwar saka dokar hana yawo a birnin Sokoto da wasu sassan jahar na tsawon sa'a 24. Ofishin mai ba gwamna shawara akan lamurran watsa labarai ne ya fitar da wannan sanarwa ranar asabar 14/05/2022. A cewar sanarwar, an dauki matakin ne don samar da zaman lafiya a jahar. Wannan nan dai na zuwa ne lokacin wata sabuwar zanga-zanga ta barke a birnin na Sokoto, wanda ke da nasaba da kamen da 'yan sanda suka yi na mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan Debirah Samuel Yakubu a Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari kwana biyu da suka gabata. In da da farko zanga-zangar da aka soma ta lumana ta rikide zuwa kone-kone. In da masu zanga-zangar suka cika harabar Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III.

An Kashe Wata Daliba Da Aka Zarga Da Batanci Ga Manzon Allah A Jahar Sokoto

Wata dalibar Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, mai suna Debora Samuel, ta gamu da ajalinta lokacin da wasu matasa da ba a kai ga sanin ko su wanene ba suka kashe ta hanyar kona ta, bayan da aka zarge ta da yin batanci ga Annabi mai tsira da amincin Allah. Lamarin ya kazance ne bayan da wasu daga daliban kwalejin suka yi zargin cewa ta dade ta na wannan batancin abinda ya kai ga barkewar rikicin da ya kai ga salwantar ranta. Tuni dai mahukuntan jahar Sokoto suka bayar da sanarwar rufe kwalejin har a kammala bincike. Babban sakatare a ma'aikatar ilmi mai zurfi ta jahar Sokoto Alhaji Almustapha Usman Ali, ya shaidawa manema labarai cewa, an bayar da umurnin rufe kwalejin kazalika za su sanar da jama'a mataki na gaba idan har an kammala bincike. An dai girke jami'an tsaro a harabar makarantar domin dakile rikicin da ka iya tasowa. Tuni dai da hotunan bidiyo da Tantabara ba ta kai ga tantantace sahihancinsu ba, suka karade shafukan sada zumunta, wadanda k...

Daliban Jahar Sokoto Ba Zasu Rubuta Jarabawar WAEC Ba

Hukumar Shirya Jarabawar Sakandire ta Afirka ta Yamma wato WAEC, ta bayyana cewa jahohin Sokoto da Zamfara ba su aike mata da sunayen dalibansu da za su rubuta jarabbawar kammala babbar sakandire ba, wadda za a soma tsakanin ranakun 16 zuwa 23 ga watan Yunin gobe, kamar yadda sakataren hukumar shirya jarabawar Mista Patrick Aregan ya fitar da sanarwa. Sai dai a hirarsa da Sashen Hausa na BBC, kwamishinan ilmi na jahar Sokoto Bello Abubakar Guiwa, ya ce matsalar ba daga gare su ba ne.  Kwamishinan ya ce hukumar ta WAEC ta fito ne da wani tsari na sun amsar kudi ba gaira ba dalili gare su wanda ya sa suka yi watsi da ita. Ya kara da cewa suna da dalibai kusan 30,000 da zasu rubuta jarabawa a wannan shekara, to amma sai hukumar hana su lambobin jarabawar da ake rabawa dalibai ta kuma ce duk wani kuskure daya da aka samu akan kowane dalibi, wajibi ne sai an biya naira 5000, wanda kuma miliyoyin kudade ne, kazalika sai gwamnatin jahar Sokoto ta biya kashi 40 cikin dari kafin...

ASUU Ta Tsunduma Sabon Yajin Aikin Watanni Uku

Kungiyar Malaman Jami'a ASUU ta fitar da wata sabuwar sanarwa a yau litinini 09/05/2022 da ta bayyana sake tsunduma wani sabon yajin aikin makonni 12. ASUU ta bayyana rashin gamsuwa da yadda bangaren gwamnatin tarayya ya dauki lamarin ba tare da muhimmanci ba. Sanarwar ta ASUU ta kuma nunar da yadda gwamnatin tarayya ta sa kafa ta shure yarjejeniyar da suka yi a 2020, tare da cewa babu wata alamar gwamnati da gaske ta ke. Kungiyar Malaman Jami'ar dai ta kwashe wata hudu tana yajin aiki kafin sake saka wani sabon wa'adi a yau na tsawon makonni 12 abinda masana harkar ilmi ke cewa ya gurgunta sha'anin ilmi a Najeriya.

Zan Yi Amfani Da Kundin Tsarin Mulki Ba Alkur'ani Ba - Yariman Bakura

Tsohon gwamnan jahar Zamfara sanata Sani Yariman Bakura ya ayyana manufarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya karkashin jam'iyyar APC. A wata hira da BBC Hausa Yariman Bakura ya bayyana cewa Najeriya na fama da matsaloli uku da zai mayarwa hankali idan aka zabe shi, da suka hada da tsaro da jahilci da talauci. Da aka tambai shi ko bai ganin wadanda ba musulmi ba na iya dari dari a zabensa. Sai ya ce a yanzu kam sabanin wancan lokaci da aka sani da kundin tsarin mulki zai yi amfani wajen rantsuwar kare Najeriya. Ya kuma kara da cewa a lokacin kaddamar da manufar tsayawarsa takara akwai limaman kiristoci daga Zamfara da wasu wurare a Najeriya da suka halarta, wanda alama ce da ke nuna zai yi ma kowa adalci a cewar sa. Sanata Sani Yariman Bakura dai shi ne gwamna na farko da ya assasa shari'ar Musulunci a jahar Zamfara a shekarar 2000. Wanda daga baya aka samu jahohin Sokoto da Kano suka bi sahu.  Abinda ya jawo karo na farko a tarihi gwamnatin jahar Zamfara ta ...

Rasha Na Shirin Kai Ma Amurka Da Kawayenta Hari

Reuters Rasha ta gargadi kasashen yammacin duniya da cewa za a dauki tsauraran matakin soji kan duk wani hari da za a kai a yankin na Rasha, tana mai zargin Amurka da manyan kawayenta da zagon kasa ga tsaron kasashen Turai ta hanyar tunzura Ukraine a fili ta kai wa Rasha hari. Yunkurin mamayar da Rasha ta yi a Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, ya raba wasu miliyoyi da matsugunansu, ya kuma haifar da fargabar kazamin fada mafi muni tsakanin Rasha da Amurka, tun bayan rikicin makami mai linzami na Cuba a shekara 1962. Watanni biyu tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine, a cikin 'yan kwanakin nan Rasha ta ba da rahoton wani jerin hare-haren da sojojin Ukraine suka kai a yankunan Rasha da ke makwabtaka da Ukraine, kuma ta yi gargadin cewa irin wadannan hare-haren na da hadari sosai. Ukraine ba ta dauki alhakin kai tsaye ba, amma ta ce abubuwan da suka faru na mayar da martani ne, yayin da Rasha ta yi kakkausar suka ga kalaman da kungiya...

Ba Mu Yarda Da Sulhu Ba - Tambuwal

Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto, wanda kuma yana daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ya yi watsi da sakamakon taron da aka yi na amincewa da mutum daya da zai tsaya takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP a 2023. Gwamna Tambuwal ya yi watsi da hakan ne ta hannun daya daga cikin kungiyoyin yakin neman zabensa, Tambuwal Campaign Organisation (TCO). A cewar wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta hannun Daraktanta, Nicholas Msheliza a ranar Juma’a ta ce “Ofishin Kamfen din Tambuwal (TCO) ya ja kunnen wani labari cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi sun fito a matsayin ‘yan takarar da za zabi daya a matsayin maslaha daga cikin mu hudu, kuma wannan karya ce tsagwaronta sannan ba daidai ba ne “Gaskiyar lamarin ita ce kungiyar ta hadu a ranar Laraba 20 ga Afrilu, 2022, a masaukin Gwamnan Bauchi da ke Abuja, inda suka yi taron bita;  kuma, gaba É—aya sun yarda cewa tsarin yarjejeniya ba ya a...

NDE Disbursed 20,000 Naira as Loan to 228 Small Scale Business Owners in Sokoto

The National Directorate of Employment (NDE) has disbursed simple rate loan of =N=20,000 to 228 small business owners in Sokoto State.   Speaking on the occasion, held Thursday, at Shamsuddeen Plaza Sokoto, the State Coordinator, Mrs Eunice J. Danmallam said the NDE was established in 1987, and since then it has continued its creative work especially for young graduates and always keeps providing training and support to small business owners.  She added that under the current Director General of the NDE, Malam Abubakar Nuhu Fikpo, a number of measures have been put in place to help youths and small scale business owners by lending them low interest loans to repay within three months.   However, Danmallan said the agency has selected about 8026 Nigerians to benefit from the Programme, of which 228 are from Sokoto State.  The Sokoto State Coordinator urged the beneficiaries of the scheme to use the loans wisely, and then demanded that ...

Abdul'aziz Yari Zai Koma PDP

A yanzu daga kowane lokaci wata majiya mai tushe ta sanar da cewa jagoran jam'iyyar APC a jahar Zamfara, kuma tsohon gwamnan jahar, Abdul'aziz Yari zai bar jam'iyyar APC zuwa PDP. Tantabara News za ta kawo cikakken. Labarin nan gaba. KUNA IYA KARANTA:  http://tantabaranews.blogspot.com/2022/03/sabon-rikici-bangaren-abdulaziz-yari-ya.html