Jami'an Ukraine da na Poland sun soki shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier da cewa yana dasawa da Rasha. Jakadan Ukraine a birnin Berlin ya kaurace wa wani bikin zaman lafiya da mawakan Rasha da Steinmeier ya shirya. Gidan rediyon DW ya ruwaito cewa, Jakadan Ukraine a Jamus Andriy Melnyk da mataimakin firaministan Poland Jaroslaw Kaczynski sun caccaki shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier sakamakon alakar da aka lura yana da ita da kasar Rasha. Melnyk ya gaya wa jaridar Tagesspiegel cewa, "Steinmeier na da abin da ya ke boyewa dangane da wannan alaka tasa da Rasha". Ya kara da cewa, "mutanen da ke da alaka da Steinmeier kamar Jens Plötner, mai ba wa Wazirin Jamus, Olaf Scholz shawara kan manufofin kasashen waje, da Sakatariyar Ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus Andreas Michaelis hadi da karin wasu, na daga cikin wadanda ake zargin cewa ba za su rasa hannu ga wannan kusanci ba". Kaczynski ya kuma bayyana cewa manufofin ketare na Jamus na da tasg...