Skip to main content

Posts

Da Dumi Dumi - An Bude Iyakokin Najeriya Hudu

Gwamnatin Najeriya ta bayar da umurnin bude kan iyakokita a yau din nan, da suka hada da ta Sokoto a garin Illela da Seme daga kudu maso yamma da Mfun ta kudu maso kudu da kuma ta Maigatari a jahar Katsina. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bayar da wannan umurnin ta hannun mai ba shi shawara kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad, wanda ya wallafa a shafinsa na tweeter. An dai kwashe fiye da shekara daya iyakokin na kulle, a bisa dalilan tsaro da hana fasa kwabrin shinkafa da miyagun kwayoyi zuwa cikin kasar. 'Yan Najeriya da dama ne suka shiga halin matsi sakamakon rufe kan iyakokin, in da tsada da karancin kayan masaruhi suka kai wani mataki da ba a saba ganin irin sa ba a Najeriya. Da dama daga kasashe makwabta da suka hada da Gana da Jamhuriyar Nijar da Kamaru, sun sha matsin lamba da a bude iyakokin domin samun damar huldar cinikayya tsakaninsu da Najeriya. Hasalima ana ganin wannan na daya daga dakilan da suka haifar da rashin jituwa tsakanin Najer...

'Yan Bindigar Da Suka Sace Dalibai A Jahar Katsina Sun Ce Kada Su Sake Jin Shawagin Jirgin Sama Kusa Da Su

A jiya ne daya daga iyayen yaran da mayakan suka dauke ya sanar da hukumomi cewa 'yan bidigar sun kira shi ta waya, in da suka yi gargadin cewa a tabbatar wani jirgin saman yaki bai sake ci gaba da shawagi a kusa da in da su ke ba, idan ba haka ba za su dauki matakin da ya yi mu su daidai. Rahotanni da ke fitowa yanzu haka na cewa maharan sun tafiyar da ta kai dazukan jahar Zamfara da yaran, kuma sun fara tattaunawa don neman kudin fansa kafin su kai ga sakin su. A yau gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari, ya sanar da manema labarai cewa, an kai ga gano yara 17 daga cikin wadanda suka tarwatse a daji, ina da tun jiya aka sada su da iyayensu. A ranar jumu'a da ta gabata dai ne wasu 'yan bindiga da ba a kai ga ganowa ba suka yi awon gaba da yaran, koda ya ke jiya litinin shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, ya bayyana cewa su suka sace yaran.

Duk Layin Kiran Da Ba A Hada Da Lambar Katin Dan Kasa Ba Za A Rufe Shi - Pantami

Ministan Sadarwar Najeriya Dakta Isah Ali Pantami ya nanata matsayarsa na tabbatar da an dakatar da sayar da layukan kira tare da tsayar da yi wa sabbin layukkan rajista. Ya bayyana hakan a lokacin taron da ya gudanar da masu ruwa da tsaki a bangaren sadarwa, da suka hada da Hukumar Da Ke Sanya Ido Kan Harkokin Sadarwa NCC da Hukumar Bunkasa Fasahar Zamani Ta Kasa NITDA da Hukumar Samar Da Katin Shaidar Zama Dan Kasa NIMC da sauran kamfunnan sadarwar wayoyin hannu na   MTN, Glo, Airtel, Etisalat ko 9mobile  da sauran su. A wajen taron ministan sadarwar ya umurci kamfunnan su kiyaye dokoki da sharuddan da aka gindaya, kazalika dukan kamfunnan sadarwar wayoyin hannu su tilasta duk mai amfani da layukansu da ya hada layinsa na kira da lambar katinsa na shaidar zama dan kasa domin tabbatar da shi. Sun kuma tattauna akan cewa za a soma wannan daga yau din nan laraba 16 ga Disamban 2020 zuwa ranar laraba 30 ga wannan watan na Disamban 2020, wanda daga nan za a rufe...

Jahohin Zamfara, Kaduna Da Jigawa Sun Bada Umurnin Rufe Makarantun Boko

Jahar Jigawa ta bayar da umurnin rufe makarantun Boko daga yau din nan laraba har zuwa wani lokacin da ba a bayyana ba. Jahohi irin su Kaduna, Kano da Sokoto sun bi sahu. Wannan mataki dai a cewar gwamnatin jahar jigawa na da alaka ne da matsalar ci gaba da yaduwar annobar korona. Amma da dama na ganin hakan bai rasa nasaba da harin da 'yan bindiga suka kai a wata makarantar kimiyya ta kwana da ke Kankarar jahar Katsina ranar jumu'ar da ta gabata ne, in da ake jin sun yi awon gaba da dalibai kusan 500. A jiya kungiyar Boko Haram ta fito ta yi ikirarin daukar alhakin sace yaran, abinda ya jefa tsoro da zullumi a zukatan al'umma.

Sanwolu Da El-Rufai Sun Killace Kan Su Saboda Covid-19

Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i ya kebe kan sa saboda wani daga cikin iyalinsa da hadimansa sun kamu da cutar korona. Gwamnan ya bayyana hakan a shafinsa na tweeter, in da ya ce a gobe lahadi zai je asibiti don auna shi a tabbatar idan har yana dauke da ita. Shi ma gwamnan jahar Legas, Babajide Sanwolu ya bayyana killace kansa sakamakon samun wasu na kusa da shi dauke da cutar. Sanwolu ya bayyana cewa wajibi ne ya kebe kan sa kafin a gudanar da gwaji, gudun kada idan ya na dauke da ita ya yadawa wasu makusanta. Jahar Legas dai na sahun gaba daga jerin masu dauke da cutar a Najeriya. Duka jahohin biyu sun yi fama da dokar kulle a watannin baya lokacin da annobar ta yi kamari. Kwanaki uku da su ka gabata an jiyo gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i, na barazanar kulle jahar muddin jama'a suka ci gaba da kin bin ka'idojin yaki da cutar korona da aka san da su.

Mutum 64 Sun Kamu Da Korona A Kaduna - El-Rufa'i

Gwamnatin jahar Kaduna ta fitar da sanarwar cewa annobar korona ta sake dawowa a jahar. Gwamnatin jahar ta tabbara da samun sabbin kamuwa da cutar har mutum 64, wanda a cewar ta tuni su ma a ka kebe su. An kuma jiyo gwamnan jahar Malam Nasiru El-Rufa'i, na cewa muddin jama'ar jahar suka ci gaba da yin biris da dokokin da aka shata musu to babu makawa gwamnatin za ta sake kulle su ruf har sai lokacin da annobar Covid-19 din ta lafa. Gwamnan ya ce yana mamakin yadda al'umma ke watsi da ka'idojin da tuni aka san da su, na rage cin koso da sanya takunkumi da kuma yawaita wanke hannuwa. Jahar Kaduna na cikin jahohin da suka fuskanci dokar kulle sakamkon barkewar annobar ta korona a watannin baya. To sai dai wannan gargadi na gwamnatin jahar ya gamu da suka, musamman ga wadanda ke kallon kalaman a matsayin na 'yan boko.

Maina Ya Kife A Kotu

 Tsohon shugaban kwamitin hana badakala a hukumar fansho ta kasa Abdulrasheed Maina, ya fadi a kotun birnin tarayya a Abuja, daidai lokacin da ake tsaka da yi masa shari'a. Tsohon shugaban kwamitin dai ana tuhumar sa ne da badakalar da ta danganci batar da kimanin naira biliyan biyu sa'adda da ya ke jagorancin kwamitin. Tun daga lokacin da aka kai shi kotu Maina ya yi batan dabo bayan da ya samu beli. Bayan kwashe tsawon lokaci ana neman sa daga bisa ni an yi nasarar gano shi a kasar Jamhuriyar Nijar. Wannan al'adar faduwa a gaban kwamitocin bincike ba bakuwa ba ce a Najeriya, in da ko watannin baya shugaban kwamitin Hukumar Raya Yankin Naija Delta (NDDC) farfesa Podei ya yi zaman tsumma a kwando, lokacin da yake amsa bahasi a gaban kwamitin majalisar wakilai na kasa dangane da badakalar da ake zargin sa da hannu na karkata kwangiloli da kudaden hukumar zuwa wata hanya daban.

Kotu Ta Aminta Da Rataye Maryam Sanda

Yau din nan kotun birnin tarayya Abuja ta tabbatar da hukunci da kotun baya ta yanke na rataye Maryam Sanda. Kotun ta bayyana cewa hukuncin da aka yanke ma ta tun da farko babu kuskure cikin sa saboda haka ta bayar da umurnin gaggauta rataye ta. An dai samu Maryam sanda da laifin kashe mijinta har lahira ta hanyar daba masa wuka. Amma ta daukaka kara kan hukuncin da aka yanke ma ta a watan Janairun wannan shekara ta 2020.

Barayi Sun Yiwa Ofishin Jaridar Daily Star Nigeria Kaf

A yau da rana wasu gungun barayi da ba a kai ga ganowa ba sun kai samame ofishin jaridar Daily Star Nigeria da ke jahar Sokoto. Babban editan jaridar, Dr. Mansur Isah Buhari ya tabbatar da wannan lamari, in da ya ce barayin sun yi awon gaba da wasu muhimman kaya da suka hada da kananan kwamfutoci, da akwatin talabijin da ma wasu kudaden da ba a bayyana adadinsu ba kawo yanzu. Dr. Mansur ya ce, "kamar yadda al'adar ofishinmu ta ke, wakilanmu na wajen nemo labarai ni kai na ma na dan fita bana wajen, lokacin da barayin suka auni hakan tare da fasa kofar ofishin in da suka wawushe kome". Jaridar Daily Star Nigeria dai na cikin na gaba gaba daga cikin jerin jaridun yanar gizo da ake da su a Nijeriya yanzu haka.

Kungiyar Boko Haram Ta Dauki Alhakin Kisan Manoma 78 A Jahar Borno

A cikin wani sabon faifan bidiyo da kungiyar ta fitar a yau, shugabanta Abubakar Shikau ya ce su ne suka aikata kisan manoman a garin Zabarbarin jahar Borno. Shikau ya ce sun yi wannan ne saboda fansa game da abinda sojojin Najeriya ke yi musu da taimakon al'umma. In da ya ci gaba da cewa da dama daga mazauna yankunan na tseguntawa jami'an tsaro maboyarsu, wanda hakan kan kai ga kama su. Shugaban kungiyar ya ce, sun dauki matakin yanka duk wanda ya ci gaba da tseguntawa jami'an sojoji sirrinsu. Har kawo yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta mayar da martani kan wannan sabuwar sanarwa da kungiyar Boko Haram ta fitar ba.