Ministan Sadarwar Najeriya Dakta Isah Ali Pantami ya nanata matsayarsa na tabbatar da an dakatar da sayar da layukan kira tare da tsayar da yi wa sabbin layukkan rajista.
Ya bayyana hakan a lokacin taron da ya gudanar da masu ruwa da tsaki a bangaren sadarwa, da suka hada da Hukumar Da Ke Sanya Ido Kan Harkokin Sadarwa NCC da Hukumar Bunkasa Fasahar Zamani Ta Kasa NITDA da Hukumar Samar Da Katin Shaidar Zama Dan Kasa NIMC da sauran kamfunnan sadarwar wayoyin hannu na MTN, Glo, Airtel, Etisalat ko 9mobile da sauran su.
A wajen taron ministan sadarwar ya umurci kamfunnan su kiyaye dokoki da sharuddan da aka gindaya, kazalika dukan kamfunnan sadarwar wayoyin hannu su tilasta duk mai amfani da layukansu da ya hada layinsa na kira da lambar katinsa na shaidar zama dan kasa domin tabbatar da shi.
Sun kuma tattauna akan cewa za a soma wannan daga yau din nan laraba 16 ga Disamban 2020 zuwa ranar laraba 30 ga wannan watan na Disamban 2020, wanda daga nan za a rufe layin duk wanda bai bi umurnin ba.
Wannan matakin da aka dauka na da alaka da kokarin magance matsalar tsaro da ke ci gaba da kamari a Najeriya.
Comments