Jahar Jigawa ta bayar da umurnin rufe makarantun Boko daga yau din nan laraba har zuwa wani lokacin da ba a bayyana ba.
Jahohi irin su Kaduna, Kano da Sokoto sun bi sahu. Wannan mataki dai a cewar gwamnatin jahar jigawa na da alaka ne da matsalar ci gaba da yaduwar annobar korona. Amma da dama na ganin hakan bai rasa nasaba da harin da 'yan bindiga suka kai a wata makarantar kimiyya ta kwana da ke Kankarar jahar Katsina ranar jumu'ar da ta gabata ne, in da ake jin sun yi awon gaba da dalibai kusan 500.
A jiya kungiyar Boko Haram ta fito ta yi ikirarin daukar alhakin sace yaran, abinda ya jefa tsoro da zullumi a zukatan al'umma.
Comments