Gwamnatin Najeriya ta bayar da umurnin bude kan iyakokita a yau din nan, da suka hada da ta Sokoto a garin Illela da Seme daga kudu maso yamma da Mfun ta kudu maso kudu da kuma ta Maigatari a jahar Katsina.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bayar da wannan umurnin ta hannun mai ba shi shawara kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad, wanda ya wallafa a shafinsa na tweeter.
An dai kwashe fiye da shekara daya iyakokin na kulle, a bisa dalilan tsaro da hana fasa kwabrin shinkafa da miyagun kwayoyi zuwa cikin kasar.
'Yan Najeriya da dama ne suka shiga halin matsi sakamakon rufe kan iyakokin, in da tsada da karancin kayan masaruhi suka kai wani mataki da ba a saba ganin irin sa ba a Najeriya.
Da dama daga kasashe makwabta da suka hada da Gana da Jamhuriyar Nijar da Kamaru, sun sha matsin lamba da a bude iyakokin domin samun damar huldar cinikayya tsakaninsu da Najeriya. Hasalima ana ganin wannan na daya daga dakilan da suka haifar da rashin jituwa tsakanin Najeriya da kasar Gana, da ta kai ga gwamnatin kasar sallamo da dama daga 'yan kasar kafin daga bisani a kai ga sasantawa.
To amma kuma, galibin jama'a na mamakin bayar da wannan umurni kwatsam, a daidai lokacin da kasar ke cikin halin tsaka mai wuya dangane da tsaro, wanda kwanan nan ma wasu mahara suka sace yara 'yan makaranta kimanin 500 a jahar Katsina, da kuma ake fargabar suna iya amfani da wanna dama don tsallakawa da yaran zuwa makwabtan kasashe.
Comments