Skip to main content

'Yan Bindigar Da Suka Sace Dalibai A Jahar Katsina Sun Ce Kada Su Sake Jin Shawagin Jirgin Sama Kusa Da Su

A jiya ne daya daga iyayen yaran da mayakan suka dauke ya sanar da hukumomi cewa 'yan bidigar sun kira shi ta waya, in da suka yi gargadin cewa a tabbatar wani jirgin saman yaki bai sake ci gaba da shawagi a kusa da in da su ke ba, idan ba haka ba za su dauki matakin da ya yi mu su daidai.
Rahotanni da ke fitowa yanzu haka na cewa maharan sun tafiyar da ta kai dazukan jahar Zamfara da yaran, kuma sun fara tattaunawa don neman kudin fansa kafin su kai ga sakin su.
A yau gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari, ya sanar da manema labarai cewa, an kai ga gano yara 17 daga cikin wadanda suka tarwatse a daji, ina da tun jiya aka sada su da iyayensu.
A ranar jumu'a da ta gabata dai ne wasu 'yan bindiga da ba a kai ga ganowa ba suka yi awon gaba da yaran, koda ya ke jiya litinin shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, ya bayyana cewa su suka sace yaran.

Comments