Skip to main content

Posts

Tsakanin Kyanwa Da Ɓeraye...

Mage ta zauna ta yi jugum ta rasa abinda ke yi mata daɗi, ko ina sai karɓar saƙon zagi da suka take yi daga dabbobin dawa da suka kiwata ta da guminsu saboda yaƙi da ɓeraye. An zargi Mage da ba wa ɓeraye damar sace daddawar jamhuriya ba tare da ɗaukar mataki ba. Ga shi kuma wa'adin mulkin Mage ya ƙare dole ta koma gefe ta zama ƴar kallo. Shin ko me Mage zata yi don kawo ƙarshen ɓarnar ɓeraye da suka tara daddawar jamhuriya don gadar kujerar Mage? Mage ta fesa fiya-fiya akan wannan daddawar miya, wanda yanzu haka ƙwari da ɓeraye suka gano Mage ta shirya ganin bayan su don haka suka haɗa kai domin yaƙar ta. A baya kowane ɓera mai riƙe da ragamar mulki ya ci karensa ba babbaka. Ya yi mulkin mallaka da kama karya. Ya saci daddawar miya son ransa, ya yaƙi duk wanda ya ɗaga masa murya, ya halatta kansa rusa akurkin kaji ba bisa ƙa'ida ba, ya mallake shingayen ƙananan dabbobi ba bisa ƙa'ida ba. Duk da babbar majalisar dokokin zartaswa ta hana su ba su yarda ba, amma a ...

DA DUMI DUMI: CBN Ya Ce Kada Bankuna Su Amshi Tsofaffin Kuɗi

'Yan sa'o'i da fitar da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar da sanarwar cewa bankuna na iya amsar tsofaffin takardun kuɗin naira 500 da naira 1000 daga hannun jama'a, to sai dai Bankin na CBN ya yi amai ya lashe in da ya ce bai amince bankuna su amshi takardun kuɗin naira ga kowa ba sai dai mutum ya kai kuɗinsa da kansa kamar yadda aka tsara da farko.

Buhari Ya Amince A Kashe Tsohuwar Naira 200

A wani jawabi da ya yi a yau Alhamis, shugaba ƙasa Muhammadu Buhari ya ba Babban Bankin Najeriya CBN umurnin sake fito da tsohuwar naira 200 a hannun al'umma domin ci gaba da amfani da ita har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun wannan shekara. Buhari ya bayyana cewa an samu muhimman nasarori ta dalilin canjin fasalin kuɗi da aka yi. Ya nunar da cewa yana sane da irin halin matsin da 'yan Najeriya suka shiga, akan haka suna iya amfani da tsohuwar naira 200 sai dai su kai tsofaffin kuɗaɗe da suka haɗa da naira 500 da kuma naira 1000 a bankin CBN. Menene ra'ayinku kan wannan batu?

CBN Insists On Deadline Despite Court Order

The Central Bank of Nigeria CBN has insisted that its February 10th deadline for the validity of old naira notes still stands. The CBN governor, Godwin Emefiele, made the disclosure while briefing the diplomatic community at the ministry of foreign affairs in Abuja. The development comes despite the ex-parte order of the Supreme Court which restrained the federal government from implementing the February 10th deadline, pending the hearing of the matter on February 15th. Emefiele said the situation is substantially calming down since the commencement of over-the-counter payments to complement ATM disbursements and the use of super-agents. He added that there is no need to consider any shift from the deadline of February 10th.

Filin Jiragen Sama Na Malam Aminu Kano Zai Ci Naira Biliyan 700

Ministan suhurin jiragen sama Alhaji Hadi Sirika, ya bayyana cewa majalisar zartaswata ƙasa ta amince da ware fiye da naira biliyan ɗari bakwai domin aikin kwangilar gyaran filin sauka da tashin jiragen na sama na duniya na Malam Aminu Kano, wanda ya ce za kammala a cikin shekara ɗaya rak. Majalisar zartaswa ta ƙasa ta kuma amince da ware naira biliyan ɗari da goma sha bakwai domin gudanar da kwangilar gina cibiyar bincike akan man fetur ta Oloibir a yankin Naija Delta. Ministan ƙasa a ma’aikatar albarkatun man fetur, Timipre Sylva ne ya shaidawa ‘yan jaridar fadar shugaban ƙasa hakan, inda ya ce za a kammala aikin kwangilar a cikin shekaru biyu da rabi. Ya ce tun a 1980 gwamnatin Alhaji Shehu Aliyu Shagari ta soma aikin, amma daga bisani aka yi watsi da shi wanda a yanzu zai zama ɗaya daga cikin manyan ayyukan da za a ci ga da tunawa da shugaba Muhammadu Buhari a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur.

Kotu Ta Tabbatar Da Peter Obi Matsayin Ɗan Takarar Jam'iyyar LP

Kotun ɗaukaka ƙara mai mazuninta a Abuja ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar APM ta shigar inda take neman a hanawa Peter Obi na jam’iyyar Labour damar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa. Waɗanda ake ƙarar su ne Hukumar Zaɓe mai zaman kanta, INEC da jam’iyyar Labour da kuma ɗan takararta Mista Peter Obi. Da ta ke yanke hukuncin tare da taimakon alƙalai uku, mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta amince da yin watsi da shari’ar a dalilin rashin cikakkun hujjoji. Alaƙalan kotun sun nemi masu saka ƙarar da su biya waɗanda ake ƙara tarar naira dubu ɗari biyu a dalilin ɓata mu su lokaci.

Tinubu Zai Dawo Da Tsoffin Kuɗi - El-Rufai

Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ya roƙi jama'a cewa kowa ya yi amfani da tsoffin kuɗi daga nan har shekara huɗu. A cikin wani gajeren bidiyo mai tsawon minti huɗu da daƙiƙa talatin da bakwai, an ga gwamnan na bayyana cewa ya bayar da umurnin duk wani ɗan jahar da ke kasuwanci kada ya fasa amfani da tsoffin kuɗaɗe. "Duk wani ɗan jahar Kaduna daga nan har shekara huɗu in dai an zaɓi APC, Uba zai mayar masa da kuɗinsa". In ji gwamna El-Rufai. A cewarsa wannan saƙo ne daga ɗan takarar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, wanda kuma in ji gwamnan da an zaɓi Tinubu zai sauya wannan tsarin canjin fasalin kuɗi nan take in da zai dawo da tsoffin da mutane ba su kai banki ba. Saboda haka ya umurci jama'a da kada kowa ya kai kuɗinsa banki. Ya ƙara da cewa da zarar an zaɓe su, ya ɗauki alkawarin amsar kuɗin mutane ya tilasta Babban Bankin Najeriya CBN ya canza su musu da sababbi. Ya ci gaba da cewa, "Ku gaya ma kowane ɗan kasuwa, ya karɓi tsohon...