Dakataccen kwamishin hukumar zaɓe na jahar Adamawa, Barista Yunusa Hudu Ari, ya ranta cikin na kare jim kaɗan bayan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi a gudanar da cikakken bincike game da badaƙalar da ake zargin sa da ita. Kakakin hukumar INEC Festus Okoye ne ya sanar da gidan talabijin na Channels haka. Okoye ya ce su kansu ba za su iya cewa ina ya shiga ba saboda tun bayan faruwar lamarin ba ya ɗaukar kiran waya kuma sun ma daina jin ɗuriyarsa gaba ɗaya. Da aka tambai shi ko akwai wani mataki da hukumar INEC za ta ɗauka kan wannan sabon lamari, sai ya ce, "ai wannan hakkin jami'an tsaron 'yan sanda ne na tabbatar da sun san inda yake. Idan har jami'an tsaro na buƙatar gurfanar da shi, su ne za su iya zaƙulo shi tare da gabatar da shi a gaban shari'a". Hudu Ari dai ya sanar da sakamakon zaɓen gwamnan jahar Adamawa a ranar Lahadin makon jiya, inda ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen tun gabanin a kammala tat...