Skip to main content

Posts

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Filato

Rahotanni sun ce an kashe mutane da dama tare da Æ™ona gidaje a rikicin da ya É“arke tsakanin manoma da makiyaya a yankin Mai Tumbi da ke Æ™aramar hukumar Mangu a jihar Filato. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni da aka tura ‘yan sanda domin tabbatar da zaman lafiya a yankin da rikincin ya shafa Babban Daraktan Hukumar Tabbatar Da Wanzuwar Zaman Lafiya a Jihar Filato Joseph Lengmang, ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya ce sun yi matuÆ™ar baÆ™in ciki da yadda lamarin ya faru, inda rahotanni masu tayar da hankali suka nuna cewa matsalar tsaro ta tabarbare a yankin, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuwa da dukiya mai É—imbin yawa.

An ÆŠaure Wani ÆŠan Jaridar Rasha Kan Sukar Putin

Wata kotu a kasar Rasha ta yankewa É—an jarida hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa zargin sa da yin kira da a hambarar da gwamnatin shugaba Vladimir Putin bayan mamayar da ya yi ma Æ™asar Ukraine a bara. Shafin yanar gizo na ‘yan shafin yanar gizo na jami'an tsaron 'yan sanda na OVD Info   ya ruwaito ranar Juma’a cewa, an kama Kirill Akimov, mai shekaru 52 a watan Yuni, bisa zargin yin kiraye-kirayen da ka iya kai wa ga tashin hankali yayin gabatar da shiri a wani gidan rediyo a ranar 14 ga Maris, 2022.  Akimov, wanda ya fito daga Jamhuriyar Mordovia ta tsakiyar Rasha, mai tazarar kilomita 400 gabas da birnin Moscow. Kotun soji da ke Yekaterinburg a ranar Laraba ta samu Akimov da laifuffuka biyu na ingiza jama'a su yi bore da kuma aikata ta’addanci, a cewar wata kotu.

Binani Ta Zama Mace Ta Farko Da AKa Zaɓa Gwamna A Najeriya

A wani abinda ba saban ba, Hukumar ZaÉ“e Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Sanata Aisha Dahiru, wacce aka fi sani da Binani a matsayin wadda ta lashe zaÉ“en gwamnan jahar Adamawa. Kwamishinan zaÉ“en jahar Adamawa, Farfesa Hudu Yunus Ari, ya ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaÉ“en ana tsakiyar tattara sakamakon zaÉ“en. An bayyana sakamako daga Æ™ananan hukumomi 10 cikin 20 yayin da aka dage ci gaba da bayyana sakamakon zaÉ“en har zuwa karfe 11 na safe. Sai dai Ari ya sanar da sakamakon Æ™arshe awa É—aya kafin lokacin da aka tsara. Gwamnan jahar Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP ne ke kan gaba kafin a bayyana hakan. Wasu magoya bayan jam’iyyar PDP a zauren sun nuna rashin amincewarsu da dalilin da ya sa kwamishinan zaÉ“e ya sanar da sakamakon maimakon baturen tattara sakamakon zaÉ“e a al'adance.

Halin Da Ake Ciki Kan Yunƙurin Juyin Mulki A Sudan

Jami'an ÆŠaukin Gaggawa don Tallafa ma Tsaro a Sudan na Rapid Support Forces (RSF) a yau asabar sun ce sun Æ™wace iko da fadar shugaban Æ™asa da gidan hafsan hafsoshin soji da babban filin jirgin sauka da tashin jiragen sama a birnin Khartoum a wani yunÆ™urin juyin mulki da aka yi a lokacin da rikici ya É“arke tsananinsu da sojoji. Rundunar ta RSF wacce ta zargi sojojin da fara kai mata hari, ta kuma ce sun Æ™wace tashoshin jiragen sama a arewacin garin Merowe da kuma El-Obeid a yammacin Æ™asar. Rundunar sojin saman Sudan na ci gaba da fatattakar mayaÆ™an RSF, a cewar wata sanarwa rundunar.   Wasu gidajen talabijin sun nuna wani jirgin soji a sararin samaniyar birnin Khartoum, amma Tantabara News ba ta tabbatar da sahihancin labarin. Rahotanni da ke shigo muna yanzu haka na bayyana cewa ana iya jin Æ™arar harbe-harbe a sassa da dama na birnin Khartoum inda wasu shaidun gani da ido da ke bayar da rahoton harbe-harbe a garuruwan da ke makwabtaka da su, lamarin da ya sa ake fa...

Iran Ta Sha Alwashin Murƙushe Masu Tallata Manufar Cire Hijabi

A ranar Asabar 15 ga watan Afrilun da ya gabata ne mataimakin babban lauyan Æ™asar Iran ya bayyana cewa, za a gurfanar da mutanen da ke Æ™arfafa mata gwiwar cire hijabi a gaban kotunan laifuka, kuma ba za su sami damar daukaka Æ™ara kan duk wani hukunci da aka yanke musu ba. Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun Æ™aruwar mata da ke bijirewa dokokin sanya hijabi da Iran ta sanya, inda suke bayyana a manyan kantuna da gidajen cin abinci da shaguna da sauran wuraren taruwar jama'a.  A cikin 'yan watannin nan wasu mata masu fafutuka sun fito fili sun yaÉ—a hotunan kansu a shafukan sada zumunta ba tare da lullubi ba. Jami'an tsaron 'yan sandan Iran a ranar Asabar É—in makon jiya, sun sanya na'urorin É—aukar hoto a wuraren taruwar jama'a don tantancewa da kuma hukunta matan da aka gano ba su sanye da hijabi, kamar yadda kafafen yaÉ—a labarai na Iran suka ruwaito.   Kamfanin dillancin kabaran Reuters ya ruwaito mataimakin babban lauyan gwamnatin Æ™a...

Wanene ÆŠan Jarida?

Ɗan jarida mutum ne kamar kowa, sai dai tunaninsa da manufofinsa kan tafi daidai ne kawai da ra'ayin MASU SAURARO ta fuskokin da suka shafi aikinsa. Ya zama mai wakiltar waɗanda ba su da baki ne ko kafafuwan zuwa, kuma idanuwan talakawa a kowane lokaci. Idan ka nuna ma sa launi shuɗi, ƙoƙarin ya ke ya tabbatar da launin nan shuɗi ne ziryan ko yana da garwaye? Idan ka ce ma sa labarin abu kaza ya faru, ba zai ce a'a ba kuma ba zai ce eh ba, aikinsa shi ne TABBATARWA . Idan mai sauraro namiji ne ko mace ko mai ra'ayin wani addini ko akida ko mai kuɗi ko talaka, ɗan jarida kan GIRMAMA kowa, kuma zai ɗauki kowa a matsayin DAIDAI ta fuskar ba su damar bayyana ra'ayoyinsu. Ɗan jarida kan tafi da zamani, ya kuma rungumi fasahar da ƘIRƘIRA ta kawo domin tafiya daidai lokaci. A kowace marra GASKIYA ita ce madogarar ɗan jarida, kuma wannan kan ƙara sa masu sauraro su amince da shi. Amma kuma, dole ne ɗan jarida ya zama MAI IKON KANSA , ba zai yi ma kowa alfarma b...

Dalar Amurka Na Fuskantar Barazanar Durkushewa

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya soki kasar Amurka akan irin rawar da dala ke takawa a tattalin arzikin duniya tare da yin kakkausar suka ga asusun lamuni na duniya na IMF. Lula ya yi waÉ—annan kalamai a wata ziyarar aiki da ya kai Chana, jiya Alhamis a birnin Shanghai a wani bikin kaddamar da takwaransa, Dilma Rousseff a matsayin sabuwar shugabar bankin raya kasashen BRICS, da gamayyar kasashenn Brazil da Rasha da Indiya da Chana da kuma Afirka ta Kudu suka samar. "Me ya sa kowace Æ™asa za a danganta da dala don kasuwanci? Wanene ya yanke shawarar dala za ta zama kuÉ—in duniya?"  Ya Æ™ara da cewa me yasa banki kamar bankin BRICS ba zai iya samun kuÉ—in da zai gudanar da hulÉ—ar kasuwanci tsakanin Brazil da Chana ba, da ma sauran Æ™asashen duniya? Ya ce yana mamakin yadda Æ™asashe cike da rauni  su ke bin sawun amfani da dala wajen gudanar da kasuwanci alhali suna iya hakan da kuÉ—aÉ—ensu. A wata ganawa tsakanin sa da shugaban Chana Xi Jinping, da kuma ya ...

Tinubu Na Gaban Tambuwal A Sokoto

Asiwaju Bola Tinubu, É—an takarar shugaban Æ™asa na jam’iyyar APC, ya ba Atiku Abubakar, É—an takarar jam’iyyar PDP a jihar Sokoto rata a jahar.   Duk da cewa akwai kananan hukumomi 23 a jihar, Tinubu ya tattara mafi yawan kuri’u a kananan hukumomi 10. Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya samu kuri’u 101,608, Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri’u 98,080 yayin da Sanata Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ya zo na uku da kuri’u 314 sannan Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu kuri’u 171. Kananan Hukumomin Da Aka Samu Sakamakonsu TURETA  WaÉ—anda aka yi ma rajita: 40,746  WaÉ—anda aka tantance: 16,516  APC 7, 684  LP.  1  NNPP.  9  PDP.  8, 144  KWARE  WaÉ—anda aka yi ma rajita 74,056  WaÉ—anda aka tantance 24,776  APC 10,485  LP.  63  NNPP.  11  PDP.  12,242  BODINGA  WaÉ—anda aka yi ma rajita 86,139  WaÉ—anda aka tantance 28,054  A 1 ...

Sakamakon Zaɓen Shugaban Ƙasa Kai Tsaye

Za mu ci gaba da kawo muku sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki na ƙasa. Hoto: BBC Hausa

An Kashe ÆŠan Takarar Jam'iyyar Labour A Kudu Maso Gabas

Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Kudu maso Gabas hatta a cikin makon da za a gudanar da babban zaÉ“en 2023. Rahotanni daga yankin sun ce wasu da ba gano ba sun kashe Mista Oyibo Chukwu, É—an takarar É—an majalisar dattawa mazabar Enugu ta gabas a ranar Asabar, sa’o’i 48 kafin gudanar da zaÉ“en. An kashe Chukwu ne tare da wasu magoya bayansa biyar a Æ™aramar hukumar Awkunanaw ta Enugu a lokacin da yake dawowa daga wani gangamin yaÆ™in neman zaÉ“e. An kuma ce masu kisan sun kona shi da magoya bayansa bayan sun tare da shi a cikin motarsa. ÆŠan takarar gwamna na jam’iyyar Labour, Chijioke Edeoga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jam’iyyun siyasa na yi wa ‘ya’yan jam’iyyarsa kisan gilla, waÉ—anda ke ganin barazana ce ga bunÆ™asar jam’iyyar a jihar. Peter Obi, É—an takarar shugaban Æ™asa na jam’iyyar Labour, ya fito ne daga yankin Kudu maso Gabas, wanda tashin hankali ya zama ruwan dare, tun kafin lokacin zaÉ“e.  Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sha alwa...