A wani jawabi da ya yi a yau Alhamis, shugaba ƙasa Muhammadu Buhari ya ba Babban Bankin Najeriya CBN umurnin sake fito da tsohuwar naira 200 a hannun al'umma domin ci gaba da amfani da ita har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun wannan shekara. Buhari ya bayyana cewa an samu muhimman nasarori ta dalilin canjin fasalin kuɗi da aka yi. Ya nunar da cewa yana sane da irin halin matsin da 'yan Najeriya suka shiga, akan haka suna iya amfani da tsohuwar naira 200 sai dai su kai tsofaffin kuɗaɗe da suka haɗa da naira 500 da kuma naira 1000 a bankin CBN. Menene ra'ayinku kan wannan batu?