Wata ‘yar jaridar wani gidan talabijin na Rasha, Marina Ovsynnikova, ta fuskanci É—aurin wata biyu saboda ta bayyana rashin goyon baya akan mamayar da Æ™asarta ke ci gaba da yi wa Yukren. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, wata kotu ta sanar da kama Ovsynnikova da laifin cin amanar Æ™asa, sakamakon É—aga kwalin da ta yi a kusa da fadar Kremlin mai É—auke da kalaman da ke cewa, “Putin mai kisan kai ne, yara nawa suka mutu sakamakon aikinka, ka gaggauta dakatar da wannan yaÆ™i”. Gwamnatin Rasha ta daÉ—e tana É—aure masu adawa da mamayar da ta ke yi ma Yukren, tare da bayyana yaÆ™in da sunan “aikin dakarun soji na musamman” kuma shugaba Putin ya sha alwashin tsare duk waÉ—anda aka samu da laifin watsa labarun Æ™arya tsawon shekara goma a gidan jarum.