Ministar kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ta ce gwamnatin tarayya ta fara lalubo zaren kawo karshen matsalar hauhawar farashin abinci a Najeriya. Ministar ta ce za a fito da wata hanyar yin taron kasa da masu ruwa da tsaki domin samar da matakin da za a dogara gare shi wajen rage ma 'yan kasa radadi cikin gaggawa. Idan ana iya tunawa gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kulle kan iyakokin kasar da zimmar bunkasa noma abinda ya haifar da tsananin tsadar abinci.