Babbar kotun daukaka kara ta kasa mai mazauninta a Abuja ta tabbatar da Alhaji Isah Sadik Achida a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jahar Sokoto. An dai shafe wata daya ana jayayya a kotu tsakanin Alhaji Isah Sadik Achida da bangaren Mainasara Abubakar da ke tare da Alhaji Abdullahi Salame sai kuma bangaren shugaban majalisar dokoki ta jahar Sokoto Hon. Aminu Manya Achida. Idan ana iya tunawa dai babban mai saka kara na kasa kuma ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami SAN, ya taba wani ikirari na cewa kotu za ta tabbatar da shugabancin ga Mainasara Abubakar da ke bangaren Hon. Abdullahi Salame, wanda wannan hukuncin ya zama tamkar watsa kasa a fuskar ministan shari'ar da ya yi riga malam masallaci gabanin hukuncin kotu.