Skip to main content

Posts

Da Dumi Dumi Manyan Sojoji Sun Mutu A Wani Hadarin Jirgin Saman Sojan Najeriya

Rahotannin da ke shigowa yanzu haka sun tabbatar da faduwar wani jirgin saman soji kirar Boeng 350, daf da filin jiragen sama na Abuja, wanda wata majiya ke cewa na kan hanyarsa ne ta zuwa Mina ta jahar Naija. Ministan suhurin jiragen sama Hadi Sirika ya tabbatar da aukuwar lamarin, ta shafinsa na tweeter, in da ya ce an samu bayanin lalacewar dayan injimini jirgin tun farkon tashinsa. Wasu bayanan na daban sun ce ana fargabar akalla mutum 14 sun hallaka da suka hada masu mukamin janar biyu, da kaftin hudu, kofura biyu hadi da ma'aikatan jirgin hudu. An dai ga wuta na ci tare da tashin hayaki da ya game wurin, a daidai lokacin da jami'an kwana-kwana ke kokarin kashe wutar.

Alamu Na Nuna Gwamna Wike Zai Shiga APC

Bayanai da ke fitowa yanzu haka na bayyana alamun gwamnan jahar Rivers Nyesom Wike na daf da tsunduma jam'iyar APC mai mulki. An jiyo babban mai tsawatawa na majalisar wakilai ta tarayya Orji Uzo Kalu na bayar da tabbacin cewa tattaunawa ta yi nisa tsakaninsa da gwamna Wike. Kalu ya sanar da manema labaru a ranar alhamis cewa, bayan da gwamnan ya gayyace shi rangadin wasu ayukka da ke gudana a babban birnin jahar Fatakwal, ne suka tattauna kan wannan batun. Orji Kalu ya kuma ce sun shafe daren ranar suna shawarwari da gwamnan akan yadda zai shigo kana ya karfafa masa guiwa kan shiga jam'iyar APC, domin jawowa jahar ta Rivers alhairai masu yawa daga gwamnatin tarayya, in da kuma ya nuna yayi na'am da wannan shawara.

Shak Ahmad Gumi Ya Fara Tattaunawa Da wadanda Suka Sace Yaran Makarantar Kagara

Malamin ya sanar da cewa maharan da suka sace daliban wata Makaranta da ke Kagaran jahar Naija, sun kira shi domin ya nemo gwamnati a tattauna yadda za a saki yaran. Shak Ahamd Gumi ya ce, shi kan sa bai san in da maharan ke fakewa ba, amma dai ya samu tattaunawa ta waya da shugaban 'yan fashin da suka addabi yankunan arewacin Najeriya, mai suna Dogo Gide, in da ya sanar da malamin alkawarin da suka dauka na tattaunawa da gwamnati. To amma kuma har yanzu bangaren gwanatin tarayya da ma jahohi ba su ce uffan ba kan wannan batu. Duk dai kokarin da jami'an tsaro na gano in da wadannan mahara ke fakewa a dazuka ya ci tura, amma a galibin lokuta Shak Ahmad Gumi ya sha kutsa kai a dazuka da zimmar ilmantar da su da kuma nan shiga tsakani don neman sulhu.  Sai dai a duk wannan kokari da Ahmad Gumi ya nuna yana yi hare-haren 'yan bindiga sai karuwa suke, inda wannan kwashe dalibai a makarantun kwana shi ne na hudu baya ga makarantar Kankarar jahar Katsina kimanin watann...

An Ruguza Makarantar Malam Abduljabbar Kano

Dazu dazun nan gwamnatin jahar Kanon ta tura jami'an ma'aikatar lura da tsarin filaye in da ta ruguza makarantar Malam Abduljabbar. Gwamnatin dai ta taba bayyana cewa filin da ya ke amfani da shi haramtacce ne, in da ta kai ga kwace shi tare da bada umurnin gudanar da wasu muhimman ayukka a wurin. Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin gwamnatin jahar Kano da Abduljabbar in da a ranar laraba sakataren watsa labaran gwamnatin jahar, Muhammad Garba ya bayar da sanarwar rufe masallacin Malam Abduljabbar tare da hana masa gudanar da wa'azi baki daya. In da ta ce hakan na da alaka da irin yadda ya ke tunzura jama'a a kalaman da ya ke amfani da su a lokacin da ya ke da'awa.

TAURARUWA MAI WUTSIYA... GANDUJE KO ABDULJABBARI?

RA'AYI: Dambarwar da ta dabaibaye batun nan na dakatar da Abduljabbar Nasiru Kabara a jahar Kano na ta jan hankalin al'umma a kwanan nan. Lamarin ya ja ra'ayin masana da masu sharhi na ta tofa albarkacin bakinsu kan batun. Wannan ya sa jaridar Tantabara News ta yi tsokaci akan yadda masana da tarihi ya hango makomar irin wadannan mutane. A ranar larabar makon jiya ne gwamnatin jahar Kano ta dauki matakin rufe masallacin da malamin ke da'awa da aka fi sani da suna As-habul Kahf da ke takiyar birnin Kano. Haka ma gwamnatin ta hana ma sa yin da'awar tare da yi ma sa wani abu mai kama da daurin talala; da ta bayyana da cewa kandagarki ne ga irin matakan da aka lura ya na dauka na hargitsa jama'a tare da boyayyar manufa mai jirwaye kama da wanka.   Wanene Abduljabbar Nasir Kabara?  Abduljabbari dai matashin malami ne mai dimbin magoya baya, mai son daukaka da suna a kafofin sada zumunta na zamani da kafar sadarwa ta YouTube mai kare mashabar Shi'a aka...

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Abduljabbar Nasir Kabara Daga Yin Wa'azi, Ta Rufe Masallacinsa

Malamin nan da aka fi sani da ra'ayi na daban da ke tsaka-tsakin mashabar Shi'a da Darika da ya ke da'awar cewa yake bi. Ya dai hadu da hushin gwamnatin jahar Kano sakamakon kalamansa da gwamnatin ta bayyana da cewa za su iya haddasa fitina a jahar. Abduljabbar Kabara dai sananne ne a kafofin sada zumunta da kuma shafukan YouTube in da ya ke watsa kalamansa da bincike ya tabbatar da sun fi karkata wajen zagin sahabbai, abinda kuma galibin jama'a da malamai suka ce ra'ayi ne irin na Shi'a. Gwamnatin dai ta bakin kwamishinan watsa labaran jahar Muhammad Garba, ta tabbatar da wannan umurnin. Ya kuma kara da cewa an ba kwamishin 'yan sandan jahar umurni da nan take ya tabbatar da an rufe masallacinsa mai suna As-habul Kaf da ke unguwar Gwale, a tsakiyar birnin Kano, tare da bayar da umurnin hana masa duk wani abu da ya kira wa'azi. Sai dai yayin da wannan umurnin ya zo a daren laraba, wasu na ganin batun bai rasa alaka da siyasa, to ...

An Gano Wani Rini Na Zamanin Annabi Dawuda

Wata jaridar kasar Isra'ila mai suna Hamodia ta wallafa labarin mai ban mamaki da ya ja hankalin duniya a makon nan. Masu hakar kayan tarihi da hadin guiwa da Jami'ar Barllan da kuma Jami'ar birnin Tel-Aviv ne suka samu nasarar gano wannan rinin mai lainin shudi, da shuni hade da saheti da aka ce ya kai shekaru dubu daya kafin bayyanar annabi Isa (a.s.) da kuma mazauna wani kwari da ake kira Slaves Hill da ke lardin Timna ke rinawa a lokacin. Wani masani na Jami'ar Barllan Dakta Naama Sukenik da Dakta Erez Ben-Yosef, sun bayyana cewa rinin, mai matukar darajar gaske an samar da kayan hadinsa ne daga kwanson dodon kodi. Kuma an wallafa bayanin a mujallar PLOS ONE .

'Yan Bindiga Sun Sako Hakimin Radda Alhaji kabir Umar

Rahotannin da ke shigowa yanzu haka, na cewa maharan da suka sace hakimin Radda, Alhaji Kabir Umar sun sako shi. Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar da sakin nasa, sai dai ba ta yi cikakken bayanin yarjejeniyar da aka cimma kafin sakin sa ba. A ranar 22 ga wannan watan na Janairun makon jiya dai ne maharan suka sace ce shi daga Katsina zuwa dajin Zamfara. 'Yan bindigar sun sako shi a daren jiya bayan kwana hudu da sace shi. Rahotanni sun ce jami'an gwamnatun jahar Katsina da hadin guiwa da jami'an tsaro sun samu tattaunawa da maharan, abinda ya kai ga sakinsa, sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa kafin sakin na sa ba.

Sabuwar Kwayar Korona Ta Bulla A Najeriya

A halin yanzu da duniya ke tsakiyar fargaba da rashin sanin makoma, Hukumar Yaki Da Cuta Mai Yaduwa ta NCDC da ke Najeriya, ta fitar da sanarwar barkewar sabon nau'in cutar annobar korona da aka lakabawa suna B.1.1.7. Wannan sabuwar kwayar cutar dai ta fi ta farko saurin yaduwa da matukar hadari wajen kashe mutane, da aka tabbatar da ta kan yadu da kashi 70 cikin dari fiye da na farkon. A watan Disamban 2020 aka samu rahoton bullar sabuwar koronar a kasar Burtaniya da Afirka ta Kudu. Shugaban hukumar NCDC ta kasa Chikwe Ihekweazu ya sanar da hakan a jiya. Ya bayyana cewa hukumar za ta kara azama don yin kandagarkin bazuwar sabon nau'in korona na B.1.1.7 tsakanin jama'a. Wani kwararren likitan Firaministan Burtaniya Boris Johnson mai suna Patrick Vallance, ya bayyana cewa, "daga marasa lafiya 'yan tsakanin shekaru 60 zuwa sama da suka harbu da tsohuwar kwayar cutar a kasar, 10 kan rasa rayukansu a cikin mutum 1000 kowace rana, amma a wannan karon, da wan...

An Rantsar Da Shugaba Joe Biden

An rantsar da shugaban Amurka na 46 Joe R. Biden tare da mataimakiyarsa Kamala Harris. Shugaba Biden ya nemi goyon bayan Amurkawa wajen samar da hadin kan kasa. "Ina neman hadin kan ku wajen ci gaba da ginin dimukuradiyarmu mai shekaru fiye da dari biyu ta ci gaba", in ji Biden. Ya kara da cewa, "Fatan da na sa gaba idan na shiga ofis, shine tabbatar da Amurka ta dore a yadda a ka santa, da inganta huldar dangantaka tsakanimu da waje, yaki da korona hadi da tabbatar da Amurka ta ci gaba da zama dunkulalliyar kasa". Shahararriyar mawakiyar nan, Lady Gaga ce ta rera taken kasar, haka ma mawakiya Jennifer Lopez ta nishandantar da mahalarta bukin. An dai gudanar da bukin cikin tsauraran matakan tsaro. Tun da safiyar yau tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bar fadar White House cikin wani jirgi mai saukar ungulu in da ya nufi jahar Florida. A can zai yi jawabin shirin kafa sabuwar jam'iyarsa da ya ce za ta samarwa Amurka makoma kasancewar manyan shugab...