Skip to main content

Da Dumi Dumi Manyan Sojoji Sun Mutu A Wani Hadarin Jirgin Saman Sojan Najeriya

Rahotannin da ke shigowa yanzu haka sun tabbatar da faduwar wani jirgin saman soji kirar Boeng 350, daf da filin jiragen sama na Abuja, wanda wata majiya ke cewa na kan hanyarsa ne ta zuwa Mina ta jahar Naija.
Ministan suhurin jiragen sama Hadi Sirika ya tabbatar da aukuwar lamarin, ta shafinsa na tweeter, in da ya ce an samu bayanin lalacewar dayan injimini jirgin tun farkon tashinsa.
Wasu bayanan na daban sun ce ana fargabar akalla mutum 14 sun hallaka da suka hada masu mukamin janar biyu, da kaftin hudu, kofura biyu hadi da ma'aikatan jirgin hudu.
An dai ga wuta na ci tare da tashin hayaki da ya game wurin, a daidai lokacin da jami'an kwana-kwana ke kokarin kashe wutar.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

An Sako Ƙarin Fasinjojin Jirgin Ƙasa Bakwai Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na ranar 28 ga Maris a jihar Kaduna sun samu 'yanci. An sako mutanen ne a safiyar Laraba bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan. Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga 'yan ta'addar domin a sako su ba. Ɗaya daga waɗanda suka shiga sasantawar mai suna Tukur Mamu, ya fada  a wata sanarwa a ranar Laraba cewa shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu.  Sanarwar ta ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani

Osinbajo Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

A jiya ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a 2023. Ya fadi hakan ne a lokacin wani kwarya-kwaryar buda baki da ya halarta tare da wasu gwamnonin jam'iyyar APC da suka hada da na jahar Kebi Abubakar Atiku Bagudo da na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i da sauran su. A yau litinin dai ne Osinbajo zai sanar da wannan kudiri nasa a dokance, ta wani jawabi da za a yada ta bidiyo. Idan ana iya tunawa dai watanni biyu da suka gabata mataimakin shugaban Najeriyar ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan manufa tasa. Kafin bayyana wannan bukata, tuni dai wasu suka fito suka bayyana bukatar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC da suka hada da tsohon gwamnan jahar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rochas Okorocha da kuma kwanan nan ministan suhuri kuma tsohon gwamnan jahar Ribas, Rotimi Amechi da sauran su.